Gabanin zaben fidda gwani: Kotu ta ba da belin Okorocha a zargin almundahanar N2.9bn da ke kansa

Gabanin zaben fidda gwani: Kotu ta ba da belin Okorocha a zargin almundahanar N2.9bn da ke kansa

  • Sanata Rochas Okorocha ya samu beli a wata babbar kotun tarayya da ke Abuja a zarginsa da ake na almundahana
  • An gurfanar da Okorocha ne a jiya Litinin kan zarginsa da wawure wasu kudade, lamarin da tun farko ya tada kura
  • An sako Okorocha a kan lokaci, daidai sadda jam'iyyar APC ke ci gaba da tantance 'yan takarar shugaban kasa na APC

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Abuja - Yanzun nan muke samun labari da duminsa daga kafar labarai ta Channels Tv cewa, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha da ke fuskantar shari'a da hukumar EFCC.

Idan baku manta ba, mun kawo rahotanni a baya da ke bayyana yadda jami'an hukumar yaki da yiw atattalin arzikin kasa ta'annuti (EFCC) suka dura gidan Okorocha kana suka tafi dashi.

Kara karanta wannan

Shirin zaben fidda gwani: Tinubu, wasu 11 sun tsallake tantancewar shugabannin APC

An ba da belin Rochas Okorocha a kotun Abuja
Yanzu-Yanzu: Kotu ta ba da belin Okorocha a zargin almundahanar N2.9bn da ke kansa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Bayan haka, aka ce an gurfanar dashi a gaban kotu, amma batun belinsa ya ci tura saboda wasu dalilai.

A rahoton baya-bayan nan, an ce daga karshe an ba da belinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Belin nasa na zuwa ne daidai lokacin da jam'iyyar APC ke ci gaba da tantance 'yan takarar shugaban kasa da suka sayi fom kwanan nan.

Okorocha na daga cikin wadanda za a tantance a yau Talata, kamar yadda wani jerin sunayen wadanda za a tantance a ranar ya nuna.

Yadda belin ya kasance

Mai shari’a Inyang Ekwo ne ya bayar da belinsa a ranar Talata a kan kudi naira miliyan 500 da kuma wanda zai tsaya masa.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya bayar da belin ne a lokacin da yake yanke hukunci kan bukatar belin Okorocha wanda a halin yanzu yake wakiltar mazabar Imo ta Yamma a majalisar dokokin kasar nan.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotu ta ba EFCC umarnin ci gaba da garkame sanata bisa zargin rashawa

Ana tuhumar tsohon gwamnan ne da tuhume-tuhume 17 da suka hada da almundahanar Naira biliyan 2.9 da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) ta shigar a kansa.

An zarge shi da hada baki da wasu da suka hada da wani dan jam’iyyar APC da wasu kamfanoni biyar domin satar dukiyar jama’a, duk da cewa ya musanta aikata laifin.

Kotu ta ba EFCC umarnin ci gaba da garkame tsohon gwamna Okorocha

Kafin nan, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare tsohon gwamnan Imo Sanata Rochas Okorocha a hannun hukumar EFCC har sai an yanke shawara kan belinsa.

Okorocha da ke a hannun EFCC, jigo ne a jam’iyyar APC, amini kana abokin harkallar tsohon gwamna, Anyim Nyerere Chinenye, rahoton The Nation.

Mai shari’a Inyang Ekwo ya ba da umarnin ne a ranar Litinin bayan da Okorocha, Chinenye da kamfanoni biyar suka gurfana a gaban kuliya bisa zarge zarge 17 na halasta kudaden haram da EFCC ta shigar.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta gurfanar da Rochas Okorocha kan zargin damfarar N2.9bn

Asali: Legit.ng

Online view pixel