Da dumi-dumi: Kotu ta umarci a kwace jami'a da otal a Kaduna na babban jami'in gwamnati

Da dumi-dumi: Kotu ta umarci a kwace jami'a da otal a Kaduna na babban jami'in gwamnati

  • Wani tsohon babban jami'in gwamnati a ma'aikatar lafiya Anthony Hassan na daf da yin asarar wasu kadarori da ya mallaka
  • Wannan dai na zuwa ne yayin da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin kwace kadarorin na wucin gadi da suka hada da jami’ar NOK da ke Kaduna
  • Ana zargin Hassan, tsohon Daraktan kudi da asusu na ma'aikatar lafiya ta tarayya ne da mallakar kadarorin daga kudaden haram

Kaduna - Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja, a ranar Laraba, 1 ga watan Yuni, ta bayar da umarnin kwace duk wasu kadarorin jami’ar NOK da ke Kaduna na wucin gadi.

A cewar wata sanarwa da hukumar EFCC ta fitar, jami’ar da tsohon Daraktan kudi da asusu (DFA) na ma’aikatar lafiya ta tarayya Anthony Hassan ya gina, ana zargin an gina ta ne daga kudaden haramun da aka gano daga mai ita.

Kara karanta wannan

Gabanin zaben fidda gwani: Kotu ta ba da belin Okorocha a zargin almundahanar N2.9bn da ke kansa

Kotu ta umarci a kwace jami'a da otal a Kaduna na babban jami'in gwamnatin tarayya
Da dumi-dumi: Kotu ta umarci a kwace jami'a da otal a Kaduna na babban jami'in gwamnati | Hoto: Economic and Financial Crime Commission
Asali: Facebook

Sanarwar da Legit.ng Hausa ta gani a shafin hukumar EFCC ta Facebook na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Hassan, wanda DFA ne a ma’aikatar tsakanin 2016 zuwa 2019 ana zargin ya gina Jami’ar ne da kudin almundahana.
“Kadarori na Jami’ar da aka kwace sun hada da ginin majalisarta, ginin ICT, rukunin gine-ginen likitanci, ginin sashen Kimiyya, gine-ginen Ilimi guda biyu, dakin karatu da sauran gine-gine.
“Sauran kadarorin da aka gano da ke da alaka da Hassan wadanda kuma aka kwace su na wucin gadi sun hada da Gwasmyen Water Factory, Gwasmyen Event Center da Gwasmyen International Hotel da ke Kaduna.”

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa Mai shari’a Zainab Abubakar, ta bayar da umarnin kwace kadarorin ne na wucin gadi yayin da take yanke hukunci kan wani kudiri da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) ta gabatar.

Kara karanta wannan

Borno: Jami'an MNJTF sun bindige 'yan ta'addan ISWAP 25, sun yi rashin jami'i 1

Lauyan EFCC, Ekele Iheanacho ya shaida wa kotun cewa EFCC ta nemi wannan umarni ne bisa ga sashe na 44 (2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya na shekarar 1999 kuma sashe na 17 na kudin zamba da sauran laifukan da suka danganci doka ta 14, 2006 da kuma ikon kotu.

A hukuncin da kotun ta yanke, kotun ta bayar da umarnin a buga wannan doka na wucin gadi a cikin jaridun kasar nan, inda ta sanar da duk mai ta cewa kan kadarorin da ya bayyana, a cikin kwanaki 14, domin kalubalantar lamarin

Mai shari’a Zainab Abubakar ta dage sauraron karar har zuwa ranar 5 ga Oktoba, 2022, domin sake duba lamarin.

Gabanin zaben fidda gwani: Kotu ta ba da belin Okorocha a zargin almundahanar N2.9bn da ke kansa

A wani labarin, yanzun nan muke samun labari da duminsa daga kafar labarai ta Channels Tv cewa, babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha da ke fuskantar shari'a da hukumar EFCC.

Kara karanta wannan

Da duminsa: EFCC ta gurfanar da Rochas Okorocha kan zargin damfarar N2.9bn

Idan baku manta ba, mun kawo rahotanni a baya da ke bayyana yadda jami'an hukumar yaki da yiw atattalin arzikin kasa ta'annuti (EFCC) suka dura gidan Okorocha kana suka tafi dashi.

Bayan haka, aka ce an gurfanar dashi a gaban kotu, amma batun belinsa ya ci tura saboda wasu dalilai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel