Ya zama na Hajiya: Mai neman aiki ya fada tarkon son shugabarsa, itama tayi caraf da abun ta

Ya zama na Hajiya: Mai neman aiki ya fada tarkon son shugabarsa, itama tayi caraf da abun ta

  • Wani dan Najeriya ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta yayin da yake bayyana auren kyakkyawar matar da ta dauke shi aiki
  • Mutumin da ke neman aiki a baya ya tattauna da matar a shafin LinkedIn amma ya fara soyayya da ita wata guda bayan tattaunawar su ta farko
  • Mutumin cikin farin ciki ya bayyana hirarsu ta farko da yadda dangantakarsu ta tashi daga shugabarsa zuwa masoyiyarsa

Najeriya - Wani dan Najeriya ya bayyana yadda dangantakar soyayya ta kullo tsakaninsa da shugabarsa ta wurin aiki.

Ademola Bhadmus ya yi amfani da shafin Twitter don bayyana bikin cika shekaru biyu na yadda ya tafi neman aiki amma ya fada soyayya da shugabarsa da kanta.

Ademola ya bayyana hirarsa ta farko da matar da ta dauke shi aiki da kuma yadda dangantakarsu ta canza zuwa ta rayuwa.

Kara karanta wannan

An Rotsa Wa Wani Kai Da Kwalban Giya a Mashaya Ya Mutu a Bayelsa

Ya yi wuff daga da shugaban kamfani daga neman aiki
Ya zama na Hajiya: Mai neman aiki ya fada tarkon son shugabarsa, itama tayi caraf da abun ta | Hoto: @Olawoyyin
Asali: Twitter

Ademola, wanda a lokacin ke neman aiki, ya tuntubi wata mai daukar ma’aikata mai suna Miriam Abubakar a kan kafar LinkedIn domin neman aiki, kamar yadda aka gani a hirar tasu mai dauke da kwanan wata 26 ga Mayu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya gaya mata cewa ya sha samun ayyuka amma bai bi ya yi su ba saboda kudin da suke biya bai taka kara ya karya ba.

Miriam ta tambaye shi irin albashin da yake so kuma ta yi alkawarin tuntubarsa idan wani abu ya taso.

Sai kuma, a cikin hira ta gaba mai kwanan watan Yuni 30, hirarsu ta canza, inda aka ga ya kira ta da 'babe.'

Martanin 'yan soshiyal midiya

@i_elkay yace:

"A ina na ajiye CV na ne? Amma mafi mahimmanci, ta yaya ka canza daga "na gode sosai" zuwa "babe" Ta yaya hakan ta faru don Allah? Ina jiran amsar ku, ina yi muku fatan alheri."

Kara karanta wannan

Dan Najeriya Da Ya Yi Digiri a Jami'ar Harvard Ta Birtaniya Ya Bayyana Sadaukarwar Da Iyayensa Suka Yi Don Tura Shi Karatu

@daddytoyosi:

"Mayu 26th zuwa 30 ga Yuni, daga sannu ranki hajiya zuwa babe. Lallai! Dangantaka ba ta da littafin taimako."

@rotilaw:

"Akwai gibi a cikin wannan labarin mana - wannan lamari ne da ba a saba gani ba - kun bar abin da ya faru tsakanin Mayu 26 da 30 ga Yuni. Canji zuwa 'babe' kwatsam."

Bidiyon yadda budurwa ta nemo tsohon saurayinta da ya haukace a Kano, ta gyara shi tsaf, ta mayar dashi gida

A wani labarin, an yi ta yabon wata budurwa a shafukan sada zumunta kan yadda ta kawo dauki ga tsohon saurayinta mai tabin hankali wanda aka ce da soja ne.

Budurwar ta san yadda tayi ta gano tsohon saurayin nata mai tabin hankali ta kuma mayar da shi gidansu da ke jihar Ribas.

A cikin wani faifan bidiyo da ta yi wanda @gossipmilltv ya yada a Instagram, an ganta a cikin wata motar bas tare da mutumin.

Kara karanta wannan

Mutumin da ya so kashe kansa ya samu kyautar N415k daga wata matashiyar mata

Asali: Legit.ng

Online view pixel