Bidiyon yadda budurwa ta nemo tsohon saurayinta da ya haukace a Kano, ta gyara shi tsaf, ta mayar dashi gida

Bidiyon yadda budurwa ta nemo tsohon saurayinta da ya haukace a Kano, ta gyara shi tsaf, ta mayar dashi gida

  • Yadda wata budurwa 'yar Najeriya ta yi wa tsohon saurayinta mai tabin hankali ya narka zukatan jama'a a shafukan sada zumunta
  • Budurwar ta ce ta gano tsohon saurayin nata da ya bata tsawon wata 4, ta gano cewa yana yawo a kan titi a matsayin mahaukaci a jihar Kano
  • Budurwar mai kyan hali ta wanke mahaukacin tas, sannan ta mayar da shi garinsu jihar Ribas a Kudancin Najeriya

An yi ta yabon wata budurwa a shafukan sada zumunta kan yadda ta kawo dauki ga tsohon saurayinta mai tabin hankali wanda aka ce da soja ne.

Budurwar ta san yadda tayi ta gano tsohon saurayin nata mai tabin hankali ta kuma mayar da shi gidansu da ke jihar Ribas.

Budurwar da ta dawo da saurayinta da ya haukace gida bayan rabuwarsu
Soyayyar gaskiya: Bidiyon budurwar da ta samo saurayinta da ya haukace a Kano | Hoto: @gossipmilltv
Asali: Instagram

A cikin wani faifan bidiyo da ta yi wanda @gossipmilltv ya yada a Instagram, an ganta a cikin wata motar bas tare da mutumin.

Kara karanta wannan

EFCC ta gano sabbin N90bn da AGF Ahmed Idris ya wawure, ya tona asirin minista da wasu jiga-jigan gwamnati

A jikin bidiyon an rubuta:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Zanje Kano neman tsohon saurayi na daya bata wata 4 saboda matsalar tabin hankali na kagu da ganinshi in kaishi gida, ina kan hanyar awanni 9, ku saka ni a addu'a."

Ta same shi a jihar Kano

Wani sabon yankin bidiyon ya nuna wani sanye da kaya a tsaftace. Da take bayyana wannan lamarin, ta bayyana cewa ta same shi a birkice a wata hanya a jihar Kano da ake kira Igbo.

Daga nan sai ta shiga motar bas da mutumin yayin da ta mayar da shi jihar Ribas wanda aka ce garinsu ne.

Budurwar ta ci gaba da yada hotunan mutumin da ke sanye da kakin soji a yayin da take zagin makiyansa da suka sanya shi hauka.

Kalli bidiyon:

Kara karanta wannan

Daga Karshe, IPOB Ta Bayyana Abin Da Ta Sani Game Da Kisar Gillar Da Aka Yi Wa Harira Da 'Yayanta 4 a Anambra

Martanin 'yan soshiyal midiya

@olatundeolajide ya ce:

"PSTD na iya haukata shi a zahiri saboda zamansa soja , ya cancanta ya zama muna taimakawa mazajen mu."

@endylight1 ya ce:

“Allah ya ba shi lafiya, da wuya a samu irinki, wannan ita ce muke kira Soyayya ta Gaskiya.
"Komai tsanani, kina tare dashi."

@polished_ice ya ce:

"Kin kyauta, amma yarinya kai shi gidan mahaukata don a kula dashi saboda yana da hadari gare ku da kansa."

@certifiedbae212 ya ce:

"Zan iya yin haka na yi kuka a ranar da na ga masoyina na farko yana tuka motar bas, na kasa hana kaina hawaye ko da ba tare muke ba ina son ganin su da farin ciki kuma masu arziki..."

Ra'ayi: Bidiyon mutumin da ya kashe N6.2m saboda ya siffanta da kare ya ba da mamaki

A wani labarin, Toko, wani masoyin kare kare ne dan kasar Japan, wanda ya nemi wani kamfani wanda ya kera masa suturar da ta canza masa kama ya koma tamkar kare.

Kara karanta wannan

Na gama Digiri amma rayuwa ta maida ni mai sayar da Gawayi, Zukekiyar Budurwa ta saki Bidiyo

Wani faifan bidiyo ya nuna mutumin da ke sanye da kayan masu siffar kare kuma hakan ya jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta tare dubban tambayoyi, inda jama'a ke son sanin abin da yasa ya dauki wannan mataki.

An ce wani kamfani mai suna Zepet ne ya samar Toko da wannan samfurin sutura mai ban mamaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel