Bidiyon Magidanci Yana Rangadawa Matarsa Mai Juna Biyu Kitso Ya Janyo Cece-kuce

Bidiyon Magidanci Yana Rangadawa Matarsa Mai Juna Biyu Kitso Ya Janyo Cece-kuce

  • Wani magidanci ya janyo cece-kuce a soshiyal midiya bayan ya rangadawa matarsa mai juna biyu kitso mai tsabar kyau
  • A bidiyon da aka wallafa a dandalin sada zumuntar zamani na TikTok, magidancin ya dauka lokaci yana tsarawa matarsa kitso wanda yayi kyau sosai
  • A martanin jama’a game da bidiyon, masu kallo sun dinga mamakin hazakarsa inda ake ayyana matarsa matsayin mai sa’a

Wani magidanci ya bai wa ‘yan TikTok mamaki bayan ya bayyana hazakarsa da ba kowa ke da irin ta ba.

Magidanci Mai Kirki
Bidiyon Magidanci Yana Rangadawa Matarsa Mai Juna Biyu Kitso Ya Janyo Cece-kuce. Hoto daga TikTok
Asali: UGC

A bidiyon, an ga matash ya dauka lokaci yana tsarawa matarsa mai juna biyu kitso kuma cike da mamaki kitson yayi kyau sosai.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai wasu mutane ba kitson bane ya birge su, hankalinsu yafi karkata da katon cikin matar inda suke cewa ai ta kusa sauke abinda ke cikin ta.

Kara karanta wannan

Rikicin Makiyaya da Manoma Ya Barke, An Yi wa Kauyuka 10 Kaca-kaca a Jihar Kano

Wasu kuwa masu son jin kwaf din a TikTok suna son sanin ko yadda ta zauna yayi mata daidai ganin tsohon cikin da take fama da shi.

A yayin martani ga duka masu luran nan, magidancin ya tabbatar da tunaninsu a sashin tsokaci inda ya bayyana cewa matarsa ta haihu jim kadan bayan yin wannan bidiyon.

A kalamansa:

“Nagode sosai abokaina da wannan yabawar. Kuma labari mai dadi shi ne bayan kwanaki uku da yI mata wannan kitson, ta haihu a ranar Asabar.”

Soshiyal midiya tayi martani

@nails_by_cheska ta tambaya:

“Shin wannan zaman yayi daidai da bayanta.”

@marydennis_43:

“Kuna ganin abinda nake gani? Babu dadewa zata haihu fa.”

@mj_njeree tace:

“A bayyane ga irin mijin da nake son aure nan amma ba zan iya fasalta shi da kalamai ba.”

@do19817 yayi martani da:

“A gaskiya wannan mutumin yana da abun mamaki. Ina taya ka murna ‘dan uwa. Allah yayi maka tsawon rai yadda zaka kula da sarauniyoyin biyu.”

Kara karanta wannan

Sarkin Shagamu Ya Makantar Da Ni Saboda Na Yi Rawa Da Matarsa, Mai Abinci

@mitchelmarila0 tace.

“‘Dan uwana, ina kamun auren ‘dan ka a nan gaba.”

@ijeleonyegboo ta kara da cewa:

“Mijina ke min kitso kuma ya wanke min kai ba tas a koda yaushe. Ina matukar kaunarsa saboda hakan.”

@hooyomacaan001 ya kara da cewa:

“A gaskiya wannan magidanci ya kai namiji. Yadda yake taimakon matarsa abun birgewa ne.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel