Zamfara: 'Yan bindiga sun sheƙe ƴan sa kai sama da 30 a Bunguɗu, sun sace shanu

Zamfara: 'Yan bindiga sun sheƙe ƴan sa kai sama da 30 a Bunguɗu, sun sace shanu

  • Tsagerun 'yan bindiga a ranar Litinin sun halaka sama da 'yan sa kai 30 a Bungudu da ke jihar Zamfara
  • Kamar yadda mazauna kauyen Gidan Dan Inna suka bayyana, 'yan bindigan sun kai hari tare da sace musu shanu masu yawa
  • 'Yan sa kai daga yankuna 10 sun taru inda suka bi su, lamarin da yasa suka musu kwanton bauna tare da yi musu kisan kiyashi

Zamfara - Wasu da ake zargin 'yan bindiga ne a ranar Litinin sun halaka sama da 'yan sa kai 30 a wani artabun da suka yi kusa da yankin Gidan Dan Inna da ke Auki a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

Mazauna yankin sun ce 'yan bindigan sun kutsa gidan Inna tun farko kuma wasu sun kai farmaki kauyuka masu makwabtaka inda suka dinga satar shanu, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Dalilin da yasa EFCC da ICPC ba za su iya gurfanar da deliget a kotu ba

Zamfara: 'Yan bindiga sun sheƙe ƴan sa kai sama da 30 a Bunguɗu, sun sace shanu
Zamfara: 'Yan bindiga sun sheƙe ƴan sa kai sama da 30 a Bunguɗu, sun sace shanu. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Sun harbe wasu mazauna yankin kuma sun tsere da shanunsu.

"Jim kadan bayan nan, shugabannin 'yan sa kai na a kalla yankuna 10 masu makwabtaka suka fara kiran mambobinsu inda suka bi sahun miyagun tare da kwato wasu shanun satan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"A cikin rabin sa'a, 'yan sa kai sun shirya kansu tare da fatattakar masu satar shanun a babura. Sai dai, a yayin da 'yan bindigan suka gane su ake bi, sai suka raba kansu kungiya biyu. Daya kungiya ta tsare shanun a cikin dajin," yace.
Ya kara da cewa, "Daya kungiyar sai ta yi kwanton bauna ga 'yan sa kai da ke kusanto su. Sun halaka sama da 30 a take saboda 'yan bindigan sun fi 'yan sa kan yawa.
"Na ga 'yan sa kai masu yawa a kan babura sun kama hanyar Gidan Dan Inna yayin da nake hanyar zuwa gona. Na yi tsammanin za a yi artabu, hakan yasa na koma gida da gaggawa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kashe ango, sun sace wasu da dama harda iyalan tsohon kwamishina a Kaduna

"Gawawwakin matattun 'yan sa kan an kwaso su domin birne su a kauyukansu. Tsoro ya cika zukatan jama'ar yankunan gudun kada su dawo su kawo wani farmakin."

Har a lokacin rubuta rahoton nan, ba a samu SP Muhammad Shehu, kakakin rundunar 'yan sandan jihar Sokoto ba a waya domin tsokaci.

Zamfara: 'Yan ta'adda sun kai farmaki kauyuka, sun halaka tare da raunata marasa kudi

A wani labari na daban, mutane bakwai ne suka halaka yayin da wasu uku suka jigata a ranar Talata, 24 ga watan Mayu yayin wani farmaki da 'yan ta'adda suka kai kauyukan Tungar-Wakaso, Dargaje, Farnanawa, Tsilligidi, Tudun-Gandu da Nannarki a kananan hukumomin Gummi da Bukkuyum a jihar Zamfara.

Miyagun wadanda aka kintata yawansu ya kai 150, sun bayyana wurin karfe 6 na yammaci, HumAngle ta ruwaito.

Wani wanda ya tsallake rijiya da baya mai suna Alhaji Maidawa mai shekaru 53 mazaunin Tungar-Wakaso, ya samu harbin bindiga a bayansa, kwauri da kafadarsa yayin farmakin.

Kara karanta wannan

Daga Karshe, IPOB Ta Bayyana Abin Da Ta Sani Game Da Kisar Gillar Da Aka Yi Wa Harira Da 'Yayanta 4 a Anambra

Asali: Legit.ng

Online view pixel