Dalilin da yasa EFCC da ICPC ba za su iya gurfanar da deliget a kotu ba

Dalilin da yasa EFCC da ICPC ba za su iya gurfanar da deliget a kotu ba

  • Deliget sun kwatanta kansu da sabbin kyawawan amare wadanda ake yayi kuma suke cin karensu babu babbaka a zamaninsu
  • An bankado yadda 'yan siyasa ke shakarawa deliget makuden kudade domin su kada musu kuri'un samun tikitin takara
  • Sai dai deliget sun bayyana cewa, EFCC da ICPC ba su da hurumin gurfanar da su saboda ba su da wata shaida kan harkallar da suka yi a zabukan fidda gwani

Wakilan jam'iyyu suna amfani da zabukan fidda gwani wurin samun kudade daga 'yan takara, inda wasu ke kwatanta kansu da kyawawan amare yayin da suke bayyana lokutan zabe da lokutan damammaki.

Sai dai 'yan Najeriya sun nuna damuwarsu kan abunda suke gani da nau'in rashawa inda suke kira da a gurfanar da deliget din.

Dalilin da yasa EFCC da ICPC ba za su iya gurfanar da deliget a kotu ba
Dalilin da yasa EFCC da ICPC ba za su iya gurfanar da deliget a kotu ba. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Daily Trust ta ruwaito cewa, a yayin jawabi wurin kaddamar da wani littafi a Abuja, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kwatanta wannan zabukan fidda gwanin da ake yi da abun takaici.

Jonathan ya ce, "Dukkan zabukan fidda gwanin da ake yi a fadin kasar nan abun takaici ne. Ba wannan bane abinda ya dace a doka. An lalata tsarin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ba za mu iya amfani da tsarin nan wurin zaben shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci da 'yan majalisar wakilai da sauransu.
"Tsarin ya lalace, wanda hakan ba abu bane mai kyau ga kasar mu. Amma za mu yi kokari mu cigaba."

Hakazalika, hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC, ta bayyana tsoronta kan yadda 'yan siyasa ke zuba kudi kan zabukan kasar nan inda suke kwatanta lamarin da yayi mai hatsari.

Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu da wanda ya gada, Farfesa Attahiru Jega, ya caccaki abinda ke faruwa.

Kungiyoyi masu zaman kansu sun bayyana wannan tsarin a matsayin rashawa mai zaman kanta. Daraktan CHRICEF, Dr Ibrahim Zikirullahi, ya ce abinda ke faruwa rashawa ce a bangaren siyasa, wacce babu shakka ta ke cire duk wani nau'in da gaskiya na zabe.

Ya ce wadanda ke da hannu wurin bai wa deliget kudi sun maye gurbin cancanta da kudi kuma suna cin banza.

Wasu daga deliget din sun ce EFCC da ICPC ba su da wata shaida da za ta sa su tuhume su.

A Kano, wani deliget ya bayyana cewa babu wani abu mara kyau tattare da karbe sulallan 'yan takara tunda kudaden ba ma dadewa za su yi ba.

"Kawai lokacin mu ne da za mu Shana. Duk wanda ke so a gurfanar da mu tabbas bai samu irin damar mu bane. Ina tantama a Najeriya idan akwai mutum daya da ba zai karba kudin ba idan na ba shi," yace.

Ya ce akasin yadda jama'a suka sakankance, deliget da yawa ba su karbar kudi kamar yadda ake yadawa, saboda akwai ta hannun wadanda kudin ke zuwa kuma suna zabtarewa kafin su bayar.

Sun tabbatar da cewa EFCC da ICPC ba su da wata shaidar ladabtar da su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel