Zamfara: 'Yan ta'adda sun kai farmaki kauyuka, sun halaka tare da raunata marasa kudi

Zamfara: 'Yan ta'adda sun kai farmaki kauyuka, sun halaka tare da raunata marasa kudi

  • Rayuka bakwai sun salwanta yayin da wasu mutum uku suka samu miyagun raunika sakamakon farmakin 'yan ta'adda
  • 'Yan ta'addan sun kai farmaki kauyukan Tungar-Wakaso, Dargaje, Farnanawa, Tsilligidi, Tudun-Gandu da Nannarki a Gummi a Bukkuyum
  • Wadanda suka tsallake rijiya da baya sun sanar da cewa 'yan ta'addan sun halaka wadanda ba su da kudi ne ko suka hana su kudadensu

Zamfara - Mutane bakwai ne suka halaka yayin da wasu uku suka jigata a ranar Talata, 24 ga watan Mayu yayin wani farmaki da 'yan ta'adda suka kai kauyukan Tungar-Wakaso, Dargaje, Farnanawa, Tsilligidi, Tudun-Gandu da Nannarki a kananan hukumomin Gummi da Bukkuyum a jihar Zamfara.

Miyagun wadanda aka kintata yawansu ya kai 150, sun bayyana wurin karfe 6 na yammaci, HumAngle ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan uwan fasinjojin jirgin kasan Abuja-Kaduna sun fito zanga-zanga a Abuja

Wani wanda ya tsallake rijiya da baya mai suna Alhaji Maidawa mai shekaru 53 mazaunin Tungar-Wakaso, ya samu harbin bindiga a bayansa, kwauri da kafadarsa yayin farmakin.

Zamfara: 'Yan ta'adda sun kai farmaki kauyuka, sun halaka tare da raunata marasa kudi
Zamfara: 'Yan ta'adda sun kai farmaki kauyuka, sun halaka tare da raunata marasa kudi. Hoto daga HumAnglemedia.com
Asali: UGC
"'Yan ta'addan sun same ni a gonata da shanu na biyu. Daya daga cikinsu dogo ne mai saiko, fari a launin fata kuma shi ne ya dube ni yace ina kudin? Na yi masa martani cikin tsoro da kaguwa cewa bani da kudi. Amma za su iya daukar shanu na," Maidawa ya sanar da tattaunawar da 'yan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Su hudu ne a wannan lokacin, kuma daya daga cikinsu ya ce ba su bukatar shanun. Ku ba mu kudi kawai. Na rantse musu cewa bani da ko kwabo a dajin nan. na roke su rangwame."

Amma ya ce 'yan ta'adda sun harbe shi sau uku yayin da yake basu hakuri kuma yayi kokarin tserewa.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun saki sabon bidiyon fasinjojin jirgin Abuja-Kaduna, cikin har da dan kasar Pakistan

"Sun harbe ni a baya. Sai nace bari induba rigar da na sagale a bishiya. Daga zuwa wurin ne na hanzarta fadawa daji, daga nan ne suka harbe ni sau biyu, a kafada da kafa."

Wani wanda ya sha da kyar ma shekaru 67 mai suna Mamman Dargaje, ya ce 'yan ta'addan sun hadu da shi yayin da yake hanyar zuwa gona.

Dargaje ya ce an harbe shi yayin da yayi kokarin kai daya daga cikin 'yan ta'addan kasa.

"Na fuskanci daya daga cikinsu wanda ya rike bindiga a kaina. Sauran sun tafi zuwa wani sashi na dajin. Na fuskancesa kuma na fi karfinsa kai tsaye," yace.
“Amma daya daga cikin 'yan ta'addan ya gan mu, kuma kafin in tsere zuwa daji, sai na ji harsashi a hakarkari na."

Mutum bakwai da aka halaka duk daga kauyen Farnanawa suke a karamar hukumar Bukkuyum ta jihar.

Harin sun tirsasa kusan mazauna kauyukan 5,000 da suka hada da mata, da tsofaffi suka bar kauyukansu. Suna kokarin karasawa Gummi da DakiTakwas domin samun mafaka.

Kara karanta wannan

Daga korafi a Facebook: Mutumin da gwamnan APC ya daure saboda sukar gwamnatinsa ya kubuta

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu, ya ce "rundunar ta aike jami'an tsaro domin shawo kan matsalar."

Ya tabbatar wa da mazauna yankin cewa za a damke duk wani mugu kuma a hukunta shi inda yayi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu.

'Yan Boko Haram sun halaka 'yan sanda 2, sun raunata wasu 5 a Borno

A wani labari na daban, a kalla 'yan sanda biyu sun rasa rayukansu yayin da waus mutum biyar suka samu miyagun raunika a lokacin da wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kai harin kwanton bauna a kan babban titin Maiduguri zuwa Damaturu a jihar Borno ranar Lahadi.

Wata majiyar tsaro ta sanar da Daily Trust cewa, 'yan ta'addan sun kai wa 'yan sandan hari ne a kauyen Goni Matari da ke tsakanain Mainok da Jakana a karamar hukumar Kaga ta jihar inda suka kone motocin sintiri biyu.

Kara karanta wannan

Rayuwar dan Adam ta yi arha a Najeriya: CAN ta yi Alla-wadai da kisan Fatima da yaranta a Anambra

"A sa'o'in farko na ranar Lahadi wurin karfe 8 na safe, 'yan ta'addan Boko Haram sun kai wa 'yan sandanmu harin kwanton bauna. Sun ajiye ababen hawansu inda suka lallaba suka shiga ta wurin kauyen Goni Matari, wanda shi ne hanyar tsallakewa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel