Daga Karshe, IPOB Ta Bayyana Abin Da Ta Sani Game Da Kisar Gillar Da Aka Yi Wa Harira Da 'Yayanta 4 a Anambra

Daga Karshe, IPOB Ta Bayyana Abin Da Ta Sani Game Da Kisar Gillar Da Aka Yi Wa Harira Da 'Yayanta 4 a Anambra

  • Kungiyar IPOB ta nesanta kanta daga kisar Harira Jubril da yaranta hudu da wasu hausawa a Anambra tana mai cewa wadanda suka yi kisan za su girbi abin da suka shuka
  • Haramtaciyyar kungiyar na masu neman kafa Biafra, ta bakin kakakinta, Emma Powerful, ta ce babban laifi ne kisar mace mai juna biyu a kasar Igbo
  • Powerful ya yi ikirarin an dauko hayan makasan fulani an turo su yankin domin su rika kisa a kuma danganta kisar da IPOB don bata mata suna

Haramtaciyyar kungiyar yan aware masu neman kafa kasar Biafra, IPOB, ta musanta cewa tana da hannu a kissar gillar da aka yi wa wata bahaushiya mai juna biyu da yaranta hudu a Jihar Anambra, rahoton The Punch.

Kungiyar ta yi Allah wadai da kisar tana mai cewa a kasar igbo, babban laifi ne kashe mace mai juna biyu. Wanda suka aikata wannan mummunan abin tabbas ta yan IPOB bane.

Daga Karshe, IPOB Ta Bayyana Abin Da Ta Sani Game Da Kissar Gillar Da Aka Yi Wa Harira Da 'Yayanta 4 a Anambra
IPOB ta ce bata da hannu a kisar Harira da yayanta 4 a Anambra. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene bane suka hallaka Harira Jubril, da yayanta hudu bayan bude musu wuta a Isulo a karamar hukumar Orumba a ranar Lahadi da ta gabata.

Yan bindiga sun kuma shiga wasu unguwannin sun halaka kimanin mutane biyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karamar hukumar Orumba ta Arewa na ciki kananan hukumomin da gwamnan Anambra, Charles Soludo ya saka dokar hana fita daga 6 na safe zuwa 6 na dare cikin sanarwar da ya fitar ranar Laraba.

Soludo ya yi tir da kisan yana mai cewa ba za a amince da hakan ba kuma ya yi alkawarin binciko wadanda suka aikata don a hukunta su.

Ba IPOB ne ta kashe Harira ba, babban laifi ne kashe mace mai juna biyu a kasar Igbo

Amma, IPOB ta bakin sakatarenta, Emma Powerful, cikin sanarwar da ta fitar a ranar Juma'a ta ce:

"Mun sha nanatawa cewa an dauko hayyan yan ta'adda an kawo su kasar Biafra su rika aikata laifuka don yunkurin bata mana gwagwarmayarmu, da bata wa IPOB suna da haramta ayyukanta, da kuma neman Birtaniya ta ayyana mu a matsayin yan ta'adda da fatan ganin ba mu cimma burin mu ba."

Powerful ya ce wadanda suka kashe bahausiyar da yaranta su saurari abin da zai biyo baya saboda zaluncin da suka yi wa matar da yaranta, rahoton Pulse.ng.

Ya jadada cewa wadanda suka kashe matar ba yan IPOB bane kuma su shirya girben abin da suka shuka.

Ya zargi sojoji da bawa Fulani masauki a barikin su tare da baki katin shaida, yana mai cewa an dakko hayan yan ta'ada ne an kawo su yankin kudu maso gabas.

'Yan bindiga sun afka wa mutane a kan titi a Kaduna, sun kashe shida

A wani labarin, wasu da ake zargin makiyaya fulani ne sun kai wa mutane da ke tafiya a hanya hari a gaban Makarantar Sakandare ta Gwamnati da ke Kagoro, Karamar Hukumar Kaura ta Jihar Kaduna.

Wani ganau, wanda ya tabbatar wa The Punch rahoton a ranar Alhamis, ya ce yan bindiga sun taho ne a kan babura sannan suka far wa wadanda suka gani.

Ya ce mutane shida ne aka tabbatar sun rasu sakamakon harin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel