Na gama Digiri amma na kare a sana'ar sayar da Gawayi, Matashiyar Budurwa ta magantu a Bidiyo

Na gama Digiri amma na kare a sana'ar sayar da Gawayi, Matashiyar Budurwa ta magantu a Bidiyo

  • Wata matashiyar budurwa da ta kammala Jami'a da takardar shaidar Digiri a fannin zane ta canza akala don samun kuɗaɗen shiga
  • A wani Bidiyo da ta tura a kafar TikTok, an hangi kyakkyawar budurwar na aikin kulla gawayi domin shirya wa kasuwa
  • Mutane da dama sun tofa albarkacin bakin su kan Bidiyon, inda suka yaba da namijin kokarinta duba da kalubalen da take fuskanta

Wata matashiyar budurwa wacce ta kammala karatu a Jami'a ta bayyana wa duniya yadda rayuwa ta canza mata duk da takardar shaidar Digiri da ta mallaka.

A wani bidiyo da ke tashe a kafar sada zumunta TikTok, budurwar ta tura Hoton ta na murnar gama karatun Jami'a da kuma bidiyonta yayin da take ƙulla gawayi na sayarwa.

Wata budurwa ta bayyana a Bidiyo.
Na gama Digiri amma na kare a sana'ar sayar da Gwayi, Matashiyar Budurwa ta magantu a Bidiyo Hoto: @salafiest10
Asali: UGC

Wata rana zaki wuce wurin

Bidiyon ya bayyana matar zaune kan kujera yar ƙarama yayin da take shirya Gawayin domin kwastomominta. Mutane da dama sun mata fatan Alheri.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Dan takarar gwamna ya janye daga takara, ya fice daga jam'iyyar APC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu na ganin cewa lokacin da tauraruwarta zata haska na nan tafe ba da jimawa ba, wasu kuma na cewa kalubalen da ta fuskanta zai zama tarihi nan gaba.

Ta rubuta a Bidiyon cewa:

"Sun ce Ilimi makullin nasara ne amma a zahirin gaskiya shi ne kwaɗon da ke garƙame nasara."

Kalli Bidiyon a nan ƙasa

Yadda mutane suka tofa albarkain bakin su

Sandy Bella ta ce:

"Komai lokaci ne, ba da jimawa ba zaki samu aikin yi, na taɓa shiga irin wannan yanayin amma kada ki karaya. Yanzu aiki jigo ne."

Jomo Inusa ya ce:

"Ina matuƙar alfahari da ke, ki yarda da ni ba zaki taba zama mai kuɗi ba a matsayin ma'aikaciya. Ma fi yawan sa'o'in mu wahala kawai suke sha. Kina kan turba mai kyau."

Eeic Nkansah ya ce:

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Tashin hankali yayin da PDP ta dage zaben fidda gwani bayan barkewar rikici

"Ɗamar samun aikin masu shaidar karatun zane ya yi ƙaranci matuƙa a Ghana."

Edna Enyonam110 ya ce:

"Amma akwai arziki a cikin wannan sana'ar nan, ni kaina ina shirin fara wa dagaske."

A wani labarin na daban kuma Dr Dikko Radda ya lashe zaben fidda gwanin APC a jihar shugaban ƙasa

Tsohon darakta Janar na SMEDAN, Dr Dikko Umaru Radda, ya zama ɗan takarar gwamnan Katsina karkashin APC.

Radda ya samu tikitin APC ne bayan zama zakara a zaɓen fid da gwanin da ya gudana ranar Alhamis da kuri'u 506.

Asali: Legit.ng

Online view pixel