Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, wasu tsagerun 'yan bindiga sun hallaka wani tsohon kwamishinan NPC
  • Wannan na zuwa jim kadan bayan kammala zaben fidda gwanin gwamna a jihar Nasarawa da ya gabata
  • Rundunar 'yan sanda ta magantu kan lamarin, ta ce tana daukar mataki domin ganin an ceto danginsa da aka sace

Jihar Nasarawa - Wasu ‘yan bindiga sun kashe tsohon kwamishinan hukumar kidaya ta kasa a jihar Nasarawa, Zakari Umaru-Kigbu, yayin da suka kai farmaki gidansa dake Azuba Bashayi a karamar hukumar Lafia.

Jaridar Punch Metro ta tattaro cewa ‘yan bindigan, wadanda suka yi harbi da misalin karfe 11:40 na daren ranar Asabar, sun kashe Umaru-Kigbu mai shekaru 60 tare da kwashe ‘ya’yansa mata guda biyu zuwa wani wurin.

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata
Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Wata majiya ta bayyana cewa marigayin wanda malami ne a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar ta Isa Mustapha Agwai da ke Lafia, ya yi aiki ne a matsayin wakilin tsohon ministan yada labarai Labaran Maku a zaben fidda gwani na gwamnan jihar Nasarawa da aka kammala.

Kara karanta wannan

Kala-Balge: Zulum ya kai ziyarar jaje ga iyalan mutane 30 da aka yanka a Borno

A cewar majiya:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Umaru-Kigbu mutum ne mai son zaman lafiya. Ya samu damar rike mukamai da dama a jihar nan. Ba mu san wanda ya yiwa laifi ba, wanda ya kai ga mutuwarsa ta fuju'a. Mun yi matukar kaduwa da samun wannan labari mai ban tausayi.”

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Ramhan Nansel, ya ce an tattara jami’ai domin dawo da zaman lafiya tare da tabbatar da ceto ‘ya’yan Umaru-Kigbu guda biyu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Nansel ya ce:

“Rundunar ‘yan sanda ta samu kiran gaggawa a daren ranar Asabar game da lamarin, wanda ya faru a Azuba Bashayi, Lafia ta Arewa.
“Nan da nan muka tura tawagar mu ‘yan sintiri sannan sojoji sun kuma tura mutanensu wurin da lamarin ya faru domin tallafa wa rundunar ‘yan sandan Najeriya domin ceto ‘ya’yansa mata guda biyu tare da cafke wadanda suka aikata wannan aika-aika.

Kara karanta wannan

Ka taimaka kada ta tayar damu daga gidajenmu: Mazauna garuruwan dake kan titin Abuja-Kaduna

“An garzaya da Umaru-Kigbu asibitin kwararru na Dalhatu Araf, Lafia, amma abin takaici, ya kasa tsira daga raunukan harsashin da aka yi masa. Ya riga mu gidan gaskiya a asibiti.”

Ƴan ta'addan ƙasar Kamaru sun shigo Najeriya, sun bindige rayuka 20

A wani labarin, tsagerun Ambazonia, wata kungiyar 'yan aware ta kudu maso yammacin kasar Kamaru, ta halaka rayuka a kalla 20 a cikin al'ummar karamar hukumar Boki ta jihar Cross River a Najeriya.

Chief Cletus Obun, tsohon dan majalisar jihar Cross River kuma dan takarar kujerar majalisar wakilai ta Boki da Ikom ne ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce lamarin ya faru ranar Lahadi.

"Zan iya tabbatar mu ku da cewa sojojin Ambazonia sun tsallako iyakar Najeriya a safiyar Lahadi inda suka kai farmaki ga wasu 'yan kasar su da suka ki shiga tsarin su."

Asali: Legit.ng

Online view pixel