Kala-Balge: Zulum ya kai ziyarar jaje ga iyalan mutane 30 da aka yanka a Borno

Kala-Balge: Zulum ya kai ziyarar jaje ga iyalan mutane 30 da aka yanka a Borno

  • Gwamnan jihar Borno ya kai ziyarar jaje ga iyalan wadanda harin Boko Haram ya rutsa dasu a makon da ya gabata
  • Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, a baya an samu wani mummunan lamari na aukuwar harin, inda aka kashe jama'a da dama
  • Gwamnan ya kuma shawarci mazauna yankin da su guji zuwa wurare masu nisa da ba kowa a yankunan jihar

Kala-Balge, Borno - Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya ziyarci karamar hukumar Kala-Balge, inda a baya-bayan nan wasu mahara suka kashe mazauna garin da dama.

‘Yan ta’addan na Boko Haram sun kai hari a wani kauyen Kala-Balge, inda suka kashe sama da mutane 30.

A ranar Lahadin da ta gabata, Zulum, wanda ya samu rakiyar Dige Muhammed, shugaban masu rinjaye na majalisar dokokin Borno, da Zainab Gimba, ‘yar majalisar tarayya, don ganawa da ‘yan uwan wadanda lamarin ya rutsa dasu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: ‘Yan bindiga sun bindige tsohon kwamishina, sun sace ‘ya’yansa mata

Yadda Zulum ya kai ziyara ga wadanda suka rasa danginsu a Kala-Balge
Kala-Balge: Zulum ya kai ziyarar jaje ga iyalan mutane 30 da aka yanka a Borno | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A nasa jawabin, gwamnan ya shawarci mazauna yankin da su daina zuwa kauyukan da ba kowa kuma masu nisa, musamman don tattara tarkacen karafa, TheCable ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa:

“Masu tada kayar bayan da abokan aikinsu sun kasance suna tattara karafa da sauran kayayyakin gida da aka jefar a kauyukan da ba kowa. Wadannan abubuwan suna aiki azaman mahadin kirkirarsu. Ina rokon ku da ku daina zuwa irin wadannan wuraren.".

Zulum ya kuma yi wata ganawa da Mohammed Jibrin, kwamandan rundunar soji da ke a Kala-Balge, kamar yadda Independent ta ruwaito.

Za a karasa wasu ayyuka a yankin

A wani bangare na ziyarar, gwamnan ya duba cibiyoyin kula da lafiya, ya kuma yi alkawarin rubanya albashin ma’aikatan lafiya masu son ci gaba da aiki a cikin al’ummar.

Ya kara da cewa:

Kara karanta wannan

2023: Dattijo ya lashe tikitin APC na sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakiya

“Duk wani ma’aikacin lafiya da yake son yin aiki a nan, za mu rubanya albashinsa, kuma za mu tabbatar da cewa, insha Allahu, za mu tabbatar da cewa an samu sauyi don ba su damar ziyartar iyalansu.”

Zulum ya kuma ba da wa'adin watanni biyu na bude asibitoci da makarantu da aka kammala, da kuma kammala ayyukan da ake gudanarwa a garin Rann, hedikwatar karamar hukumar.

'Yan Boko Haram sun yanka manoma 45 a wani sabon harin Borno

A tun farko, mazauna garin Rann, kauyen iyaka a jihar Borno, sun ce da tsakar ranar Litinin, 23 ga watan Mayu, sun yi jana'izar akalla 45 daga cikin 'yan uwansu da aka kashe a wani hari da wasu 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne suka kai wa yankinsu.

Mazauna yankin da suka shaida lamarin sun shaidawa HumAngle cewa suna ci gaba da lalume a ciyayi da ke kusa da su don gano gawarwakin da har yanzu ba a samu ba.

Kara karanta wannan

Ka taimaka kada ta tayar damu daga gidajenmu: Mazauna garuruwan dake kan titin Abuja-Kaduna

Rann, hedkwatar karamar hukumar Kala Balge ce, kuma ita ce garin da aka fi tunawa da shi da munanan abubuwan da suka faru na mace-mace a sanadiyyar 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel