Ka taimaka kada ta tayar damu daga gidajenmu: Mazauna garuruwan dake kan titin Abuja-Kaduna

Ka taimaka kada ta tayar damu daga gidajenmu: Mazauna garuruwan dake kan titin Abuja-Kaduna

  • Al'ummar garin Rijana, Katari da Akilibu sun yi kira ga Gwamna El-Rufa'i kada ya tayar da su daga garuruwansu
  • Titin Kaduna zuwa Abuja ya zama hanya da yafi kowani hanya a Najeriya hadari sakamakon hare-haren yan bindiga
  • Malam Nasir El-Rufa'i ya bada shawaran tayar da wasu garuruwa uku dake kan titin la'alla a samu tsaro

Kaduna - Mazauna garuruwa uku dake hanyar Abuja zuwa Kaduna sun mika kokon bararsu ga Gwamna Nasir El-Rufa'i na jihar Kaduna kada ya tayar da su daga muhallansu.

Garuruwan uku sun hada da Akilibu, Rijana da Katari.

Shugaban garurwan, Magaji Danjuma-Katari, ya mika wannan roko ga gwamnan ne a hira da manema labarai ranar Juma'a a Kaduna, rahoton Daily Nigerian.

Yace:

"A iyakan saninmu, al'ummarmu basu da masaniya kan wani mutum guda wanda aka kama yana aikin yan bindiga."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun sace malamin addini da wasu mutane 7 a jihar Katsina

"Saboda haka zargin karyan da ake mana cewa muna hada baki da yan bindiga soki burutsu ne kuma bai da tushe."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Sabanin karerayin da wasu ke yi mana, mazauna garuruwan na cikin wadanda yan bindiga suke addaba."

Abuja-Kaduna
Ka taimaka kada ta tayar damu daga gidajenmu: Mazauna garuruwan dake kan titin Abuja-Kaduna
Asali: UGC

Ya yi bayanin cewa wata hanyar dake masu kiwo ke bi ya wuce ta Katari shiyasa yan bindigan ke cin karansu ba babbaka.

Mr Danjuma-Katari ya yi kira da gwamnati ta duba dukkan rahotannin tsaro kan garuruwan don tabbatar da cewa ba rade-radi bane kawai.

El-Rufa'i ya bada shawarar tayar da wasu garuruwa uku dake kan hanyar

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Alhamis da ta gabata ya bada shawaran tayar da kauyukan Katari, Rijana da Akilibu, dake kan titin babbar hanyar Kaduna-Abuja.

Yace masu kaiwa yan bindiga bayanai ne suka cika wadannan kauyuka.

Kara karanta wannan

Zamfara: 'Yan ta'adda sun kai farmaki kauyuka, sun halaka tare da raunata marasa kudi

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne yayin karban rahoton irin hare-haren yan bindigan da jihar Kaduna ta fuskanta tsakanin watar Junairu da Maris, rahoton TheNation.

Ya ce yanzu yan ta'adda sun tashi daga Arewa maso gabas, sun shiga Arewa maso yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel