Mutuwa dai dole ce: Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta riga mu gidan gaskiya

Mutuwa dai dole ce: Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta riga mu gidan gaskiya

  • Duniya dai dole a mutu, mace mafi tsufa a duniya Kane Kanaka ta bakunci kiyama bayan shafe shekaru 119 a duniya
  • Kwanan nan Kane Tanaka 'yar kasar Japan ta yi bikin zagayowar ranar haihuwarta kuma a cewar danginta, ta kasance tana ciki da waje a asibiti kafin ta ci taliyar karshe
  • Toshuwa dai na kunyar a kira ta wacce tafi tsufa a duniya, taken da wata mata Bafaranshiya, Jeanne Louise Calment ta rike wacce ta rasu tana da shekara 122

Japan - Matar da ta fi kowa tsufa a duniya a karshe dai ta bar duniyar; Kane Tanaka ta rasu a ranar 19 ga Afrilu, 2022 tana da shekaru 119.

Babban kwararre kan ilimin tsufa da lafiya (Gerontology) Robert Young ne ya ba da labarin mutuwarta, wanda kuma ya taka rawa wajen tabbatar da ba da rahoto kan Kane a matsayin mafi tsufa a duniya a 2019.

Kara karanta wannan

Farinciki ya zama bakin ciki: Bidiyon amarya da ta haukace ranar aurenta

Matar da ta fi kowa shekaru a duniya
Mutuwa dai dole ne: Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta riga mu gidan gaskiya | Hoto: @tanakakane0102, Junko Tanaka
Asali: UGC

A ranar 13 ga Afrilu, dangin Kane sun yi rubutu a Twitter cewa an kwantar da ita a asibiti kuma akan sallame ta kana ta dawo.

Kundin tarihin duniya na Guinness ya ruwaito cewa an haifi Kane a ranar 02 ga Janairu, 1903, a matsayin diya ta bakwai ga Kumakichi da Kuma Ota.

Tsohuwar ta kasance a wani gidan hutawa a Fukuoka kuma inda take wasan alluna da yin lissafi

Kundin na Guinness ya ba ta takardar shaidar tsufa, kana da kyautar cakuleti a wani biki.

Wani sako da danginta suka yada a Twitter game da samun takardar sun ce ta ce:

"Na sami damar zuwa wannan nisa ne tare da goyon bayan mutane da yawa. Ina fatan za ku ci gaba da nishadi, kuma ku kasance cikin fara'a da kuzari."

Kara karanta wannan

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

Mai rikon fitar Olympic Tokyo a 2020

An zabi Kane a matsayin daya daga cikin masu rike da fitilar Tokyo 2020 na Torch Relay amma bata samu halarta ba saboda Korona.

Tsohuwar dai na kan hanyar zama mafi tsufa a cikin matan duniya, lakabin har yanzu mallakar wata Bafaranshiya ce, Jeanne Louise Calment wacce aka haifa ranar 21 ga Fabrairu, 1875, kuma ta rasu a ranar 04 ga Fabrairu, 1997, tana da shekaru 122 da kwanaki 164.

Mutumin da ya fi kowa tsufa a duniya shi ne Jiroemon Kimura dan kasar Japan wanda aka haife shi a ranar 19 ga Afrilu, 1897, kuma ya rasu yana da shekaru 116 da kwana 54, a ranar 12 ga Yuni, 2013.

An kashe mutum uku a wani rikicin yan daba kan budurwa a jihar Kwara

A wani labarin daban, mutum uku sun rasa rayuwarsu, wasu da dama sun jikkata ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Offa ta jihar Kwara sanadin wata budurwa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

Daily Trust ta rahoto cewa kungiyoyin yan daba biyu ne suka gwabza da juna biyo bayan wani saɓani da suka samu kan mace.

Rahoto ya nuna cewa faɗan ya soma ne ranar Asabar. Wani mazaunin yankin, Alhaji Abdurrahman, ya shaida wa jaridar cewa faɗan ya kaure ne tsakanin yan daban tsagin Isale Oja da na tsagin Oja Oba a Offa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.