An kashe mutum uku a wani rikicin yan daba kan budurwa a jihar Kwara

An kashe mutum uku a wani rikicin yan daba kan budurwa a jihar Kwara

  • Mutum uku sun rasa rayuwarsu yayin da wani faɗa ya kaure tsakanin yan daba kan budurwa a jihar Kwara
  • Bayanai sun nuna cewa lamarin ya fara ne yayin da shugaban tsagi ɗaya ya kwace wa abokin hamayyarsa budurwa
  • A sanarwan da hukumar yan sanda ta fitar, ta tabbatar da mutuwar mutum biyu, kuma jami'ai na cigaba da bincike

Kwara - Mutum uku sun rasa rayuwarsu, wasu da dama sun jikkata ranar Lahadi a ƙaramar hukumar Offa ta jihar Kwara sanadin wata budurwa.

Daily Trust ta rahoto cewa kungiyoyin yan daba biyu ne suka gwabza da juna biyo bayan wani saɓani da suka samu kan mace.

Rahoto ya nuna cewa faɗan ya soma ne ranar Asabar. Wani mazaunin yankin, Alhaji Abdurrahman, ya shaida wa jaridar cewa faɗan ya kaure ne tsakanin yan daban tsagin Isale Oja da na tsagin Oja Oba a Offa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wani Bam ya ƙara fashewa a babban birnin jihar Arewa, ya shafi mutane da dama

Taswirar jihar Kwara.
An kashe mutum uku a wani rikicin yan daba kan budurwa a jihar Kwara Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

A cewarsa, shugaban ɗaya daga cikin kungiyar yan Daban ne ya kwace budurwan mamban ɗaya kungiyar 'yan daban da suke hamayya da juna, hakan ya jawo faɗa.

Wane mataki hukumomin tsaro suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar Kwara, SP Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da mutuwar mutum biyu daga cikin yan daban, inda ya ƙara da cewa a halin yanzun suna kan gudanar da bincike.

A wata sanarwa da ya fitar, kakakin yan sandan ya ce:

"Kafin isar jami'an 'yan sandan da aka tura zuwa wurin da abun ke faruwa. biyu daga cikin yan daban da basa ga maciji da juna, Samad Adeyemi, 21, da Abdulahi Mohammed, 20, sun rasa rayuwar su."
"A halin yanzun dakarun yan sanda na cigaba da gudanar da bincike kan lamarin."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wasu yan bindiga sun saki sabon Bidiyo, sun yi barazanar hana zaɓen 2023

A wani labarin na daban kuma wani abun fashewa da ake zaton Bam ne ya ƙashe mutum ɗaya wasu da dama sun jikkata a Yobe

Wani abun fashewa ya yi ajalin mutum ɗaya, wasu kusan Bakwai sun jikkata a garin Gashua, hedkwatar karamar hukumar Bade a Yobe.

Wani mai shago a kusa da wurin da abun ya faru, Abdu Sherrif, ya ce suna cikin Sallar Isha'i suka jiyo tashin abun fashewar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel