Abin da Ake Zargi Ya Tabbata, Jagoran Ƴan Bindiga Ya Faɗi dalilansu na Ɗaukar Makami
- Wani jagoran ’yan bindiga mai suna Babangida ya ce shekaru da dama ana zaluntar Fulani makiyaya, lamarin da ya tilasta wasu cikinsu shiga harkar ta’addanci
- Ya bayyana cewa ya shiga harkar ’yan bindiga ne bayan jami’an tsaro sun kwace shanunsa 97, tare da tilasta masa biyan miliyoyin naira kafin sakin iyalansa
- Kwamishinan tsaron cikin gida na Katsina ya amince cewa zalunci na daga cikin abubuwan da ke haddasa ayyukan ta’addanci a Arewa maso Yamma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Wani jagoran ’yan bindiga ya bayyana cewa shekaru da dama ana nuna wariya da zalunci ga Fulani makiyaya, lamarin da ya ce ke ƙara rura wutar rashin tsaro
Jagoran ’yan bindigar mai suna Babangida ya ce matsalar za ta ci gaba da ƙamari muddin hukumomi ba su magance cin hanci da rashawa da rashin adalci da suka dabaibaye yankin ba.

Kara karanta wannan
Kwana 2 kafin ziyarar Tinubu, 'yan bindiga sun kewaye gari sun buɗe wa mutane wuta

Source: Facebook
Dan bindiga ya yi tone-tone
Babangida ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Faransa, AFP, wanda Vanguard ta bibiya.
Arewa maso Yamma da wasu sassan Arewa ta Tsakiya sun shafe shekaru suna fama da ayyukan ƙungiyoyin ’yan bindiga, waɗanda ke kai hare-hare kauyuka, satar shanu, garkuwa da mutane da kuma karɓar haraji daga manoma da masu haƙar ma'adinai.
A cewarsa, zaluncin da ake yi wa Fulani makiyaya ne ya sa wasu daga cikinsu suka shiga harkar ’yan bindiga.
“Abubuwan da suka faru na rashin adalci tsawon shekaru ne suka tilasta wa Fulani makiyaya shiga harkar ’yan bindiga. A baya ba mu kasance masu aikata laifuka ba."
- In ji shi.
Yadda rikicin makiyaya da manoma ya fara
Rikicin ’yan bindiga ya samo asali ne daga saɓani tsakanin makiyaya da manoma kan amfani da filaye da wuraren samun ruwa, wanda sauyin yanayi da ƙaruwar al'umma suka ƙara tsananta.
Daga baya, rikicin ya haifar da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, waɗanda galibinsu suka fito daga cikin Fulani makiyaya.
Abin da ya fara a matsayin hare-hare da ramuwar gayya tsakanin manoma da makiyaya ya rikide zuwa manyan ayyukan ta'addanci da laifuffuka.
Wasu daga cikin ƙungiyoyin sun ƙirƙiri sana'ar garkuwa da mutane, inda suke samun ɗaruruwan dubban daloli daga kuɗin fansa, wasu sun kulla alaƙa da ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi a Najeriya.
Babangida ya ce ya amince da tattaunawar ne bayan shafe watanni ana ƙoƙarin shawo kansa, tare da taimakon wani tsohon jami'in gwamnati da ke shiga tsakani wajen sasanta rikice-rikice.
Ya ce:
“Adalci ne kaɗai hanyar fita daga wannan matsala. Idan aka tabbatar da adalci, kowa zai zauna lafiya."

Source: Original
Yadda ya shiga ta'addanci bayan kwace masa shanu
Babangida mai shekaru 38 ya bayyana cewa ya shiga harkar ’yan bindiga ne kimanin shekaru 10 da suka gabata bayan wasu jami’an ’yan sanda da ’yan sa-kai sun kwace shanun iyalinsa guda 97.
Ya ce an kwace shanun ne bisa zargin cewa dukkan Fulani masu kiwo ’yan bindiga ne, sannan an tilasta masu biyan miliyoyin Naira domin samun belin mahaifiyarsa da ɗan’uwansa da aka kama.
Sai dai bayan biyan kuɗin, ya samu shanu 10 kacal daga cikin 97 da aka kwace, ya ce daga cikin shanun 10 da ya samu ne ya sayar da wasu domin sayen makamai.
“Na yi amfani da su wajen sayen bindigogi, ɗaya daga cikinsu ita ce wadda nake riƙe da ita yanzu,”
- in ji shi.
Ya koka kan wariyar da ake yi wa Fulani
Fulani makiyaya sun shafe tsawon shekaru suna kiwo, inda suke ƙaura daga yankunan Arewa masu bushewar ƙasa zuwa yankunan Arewa ta Tsakiya da Kudancin Najeriya a lokacin rani.
Sai dai matsalolin hamada, sare bishiyoyi, sauyin yanayi, ƙaruwar al'umma da faɗaɗa gonaki sun ƙara haifar da rikici tsakanin manoma da makiyaya.
A wasu lokuta, shanun makiyaya kan shiga gonaki su cinye amfanin gona, lamarin da ke haifar da rikici tsakanin ɓangarorin biyu.
Babangida ya zargi wasu shugabannin ƙauyuka da jami'an tsaro da haɗa baki da manoma wajen zaluntar makiyaya, cewar Punch.
Kwamishinan tsaron Katsina ya amince da zargin
Sai dai Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Katsina, Nasiru Mu'azu, ya amince cewa rashin adalci na daga cikin abubuwan da ke haddasa matsalar.
Da yake magana kan zargin Babangida, Mu'azu ya ce:
“Yana da gaskiya. Ba za ka iya ware wannan matsala daga cikin abubuwan da ke haddasa aikata waɗannan laifuffuka ba.”
Ya bayyana cewa gwamnatin jihar Katsina ta yi ƙoƙarin ƙaddamar da tattaunawar zaman lafiya domin magance matsalolin da ke haifar da rashin tsaro.
An kashe hatsabibin dan bindiga a Katsina
An ji cewa rahotanni sun bayyana cewa an kashe fitaccen jagoran ’yan bindiga yayin musayar wuta tsakanin ƙungiyoyin ’yan bindiga a jihar Katsina.
An ce lamarin ya faru ne a wani daji da ke ƙaramar hukumar Faskari a yammacin ranar Litinin 9 ga watan Nuwambar 2026.
Wani manazarci kan harkokin tsaro ya bayyana cewa marigayin ya shahara wajen satar manoma tare da tilasta musu yin aiki a gonakinsa.
Asali: Legit.ng


