Farinciki ya zama bakin ciki: Bidiyon amarya da ta haukace ranar aurenta
- Ranar da ya kamata ta zama ta farinciki a rayuwar wata amarya ta juye zuwa ranar bakin ciki, yayin da budurwa ta haukace a ranar aurenta
- A halin yanzu, bata iya tafiya daidai, budurwar mai shekaru 38 mai suna Faina ta koma rarrafe bayan ta farfado daga cutar haukar da ta kama ta a ranar bikinta
- A yanzu, danginta na neman taimako daga jama'a masu tausayi da jinkai da su taimakawa Faina wajen samar mata da keken guragu
Wasu iyaye 'yan kasar Rwanda na neman taimako daga al'umma da su taimaka wajen siya wa 'diyarsu 'yar shekara 38, mai suna Faina keken guragu.
Labarin Faina shine na budurwar da ta fuskanci matsanancin juyin rayuwa bayan ta haukace a ranar aurenta, shekaru 18 da suka shude.
Yayin zantawa da Afrimax, mahaifinta mai shekaru 75, mai suna Nzanzufwimo Kaitan ya bayyana yadda aka haifi 'diyarsa, wacce ita ce mai daukar ragamar iyalin lafiya lau, kuma take takawa da kafafunta, amma a yau ta koma rarrafe.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Faina ta koma rayuwa a birni don neman abun rayuwa, bayan gaza karasa karatunta saboda rashin kudi.
Ta samu aiki a birnin a matsayin 'yar aikin cikin gida, hakan yasa ta zama mai daukar nauyin danginta saboda yadda ake biyanta da kauri.
Daga nan ne budurwar ta hadu da wani mutumi, wanda ya sace zuciyarta.
A lokacin ne budurwar mai shekaru 20 ta koma kauye don fara shirye-shiryen bikin aurenta, daga nan ne matsalarta ta fara.
Bikin Faina bai yuwu ba
Mahaifinta ya bayyana yadda wani mummunan lamari ya auku a ranar aurenta.
"Ta fara ciwon kai, ganin jiri daga nan sai ta haukace ta bi titi tana gudu. Shikenan ta daina magana, kuma ta daina tafiya, sai ta fara rarrafe."
Hakan yasa aka garzaya da ita asibiti, gami da dakatar da batun aurenta.
Budurwar ta warke amma abubuwa suka kara tsananta
Yayin bada labari a kan mummunan lamarin da ya auku a wannan bakar ranar, Yayar Faina mai suna Mushimiyimana Alphonsine, wacce ke ganin asiri aka wa 'yar uwarta ta ce:
"A lokacin da muke shirye-shiryen shagalin bikinta, sai ta fara ciwo. Daga nan ne kafafunta suka kanannade, hakan yasa ta daina tafiya gaba daya."
Wanda a da shine zai aureta ya yi aure bayan shekaru uku da aukuwar lamarin, inda a halin yanzu yake da 'ya'ya biyu.
Masu amfani da kafafan sada zumuntar zamani sunyi tsokaci
Clauronica ta ce: "Mutane azzalumai ne, ina fatan Ubangiji zai dubi lamarinta! Mata dake aure, ku tuna da cewa, wasu daga cikin 'yan uwanku basa murna da hakan, saboda haka ku nemi maganin tsari a ranar aurenku!"
Grace Forpurpose ta ce: "Da izinin Ubangiji sai makiyanki sun amsa zaluncinsu,, Ubangiji ya taya ki yaki yadda makiyanki ba za su yi nasara a kan ki ba. Ubangiji ka kawo dauki ga diyarka da sunan Yesu."
Regina Akuamoah Boating ta ce: "Ana bukatar tsananin addu'a kafin, yayin da kuma bayan aure. Lallai duniya abun tsoro ce yanzu. Ubangiji ya warkar da ita."
God's beloved ya ce: "Rayuwa cike da almara take. Duk abunda muke gani ba shi bane. Ubangiji ya taimakesu su yi nasara a wannan yakin daga sihiri."
Asali: Legit.ng