Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden

  • Kasar China ta yi Allah wadai da lamarin kona Al-Qur'ani mai girma da wasu suka yi a kasar Sweden
  • Kakakin ma’aikatar harkokin waje na kasar China, Wanga Wenbin, ya yi kira ga kasar ta Sweden a kan ta mutunta Musulmai marasa rinjaye a cikinsu
  • Ya kuma ja hankalinta kan cewa yancin yin magana ba yana nufin a ci zarafi ko nuna wariya ga wani ba

China - A ranar Laraba, 20 ga watan Afrilu ne kasar China ta caccaki Sweden bayan faruwar wani al’amari a kwanan nan wanda ya shafi kona Al-Qur’ani mai girma, jaridar The News ta rahoto.

A wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin waje na kasar China, Wanga Wenbin ya fitar a ranar Laraba, ya bukaci Sweden da ta mutunta musulmai da addininsu.

Kara karanta wannan

Buhari ga 'yan Boko Haram: Ba zai yiwu ku dunga kashe bayin Allah kuna kabbarta 'Allahu Akbar' ba

Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden
Kin jinin Musulmi: China ta yi Allah wadai da wadanda suka kona al-Qur'ani a Sweden Hoto: Associated Press Of Pakistan
Asali: UGC

Wenbin ya ce:

"Yancin fadar albarkacin baki ba hujja ba ne da zai sa a ci zarafin wani ko kuma nuna wariya wanda ke raba kan al'umma.
"Muna fatan Sweden za su mutunta musulmai marasa rinjaye da addininsu."

Sashin Hausa na BBC ya rawaito cewa a watan jiya ne, Paludan Rasmus, shugaban masu tsattsauran ra'ayi ya kona Qur'ani a Linkoping, da ke Sweden. Sannan ya kuma ya yi barazanar cewa zai kona wasu littatafai na daban.

Kasashen Turkiyya, Saudiyya da sauran kasashen Larabawa da na musulmi da dama da kungiyoyi sun yi Allah-wadai da wulakanta littafin mai tsarki.

Sun bayyana hakan a matsayin tunzurarwa da tsokanar al’umman musulmi.

Kungiyar hadin kan kasashen musulunci na daga cikin wadanda suka yi kakkausar suka ga lamarin.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Jirgin saman sojoji ya hatsari a Kaduna, jami'ai 2 sun mutu

Zanga-Zanga Ta Ɓarke Bayan Wani Ɗan Siyasa Mai Ƙyamar Musulunci Ya Ƙona Al-Ƙur'ani Mai Tsarki

A baya mun ji cewa birnin Linköping da ke gabar tekun gabashin Sweden ya rikice sakamakon wata hayaniya da ta hautsine tsakanin masu zanga-zanga don nuna fushinsu akan kona Al-Kur’ani mai girma da wani dan siyasa mai nuna tsana ga addinin musulunci ya yi da kuma ‘yan sandan kasar.

Kamar yadda BBC ta nuna, ‘yan sanda uku sun jigata sakamakon rikicin.

Hukumomin birnin Orebro da ke tsakiyar kasar sun nuna yadda mutane suka sake fita zanga-zangar bayan wani dan siyasa, Rasmus Paludan ya shirya gangamin nuna tsana da kyama ga bakaken fata da addinin musulunci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel