Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa

  • Hukumar NDLEA ta kame wasu da suka hada casun busa tabar wiwi a babban birnin tarayya Abuja
  • Hukumar ta bayyana cewa, akalla mutum 200 ne suke hannu, ciki har da wasu mata uku da suka hada bikin
  • Wannan na zuwa ne yayin da hukumar NDLEA ke kara kauri wajen kassara lagon sha da fataucin miyagun kwayoyi

Asokoro, Abuja - Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) sun kai samame a wani wurin casu da ke unguwar Asokoro a babban birnin tarayya, tare da cafke wasu mutane.

Kakakin hukumar, Femi Babafemi, ya tabbatar wa da jaridar Punch faruwar lamarin a safiyar ranar Alhamis.

A cewar Babafemi, bikin casun da ake magana akai wasu mata uku ne suka shirya shi, kuma ya faru ne a daren Laraba.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojin Najeriya sun sake kama kasurgumin dan leken asirin Boko Haram

Jami'an NDLEA sun yi babban kamu
Da dumi-dumi: NDLEA ta kai samame wurin bikin casu a Abuja, ta cafke jama'a da yawa | Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta tattaro daga majiyar cewa hukumar ta shiga yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi a kasar nan.

Duk da cewa Babafemi bai tabbatar da adadin mutanen da aka kama ba, wani a shafin Twitter da ya halarci casun a lokacin da aka yi kamen ya tabbatar da cewa an kama sama da mutane dari.

Mutumin da ya wallafa hahan a shafinsa na Twitter, @Ezioimmauel, ya ce kusan dari daga cikinsu aka kama nan take.

Jaridar ta Punch ta ce , ya wallafa cewa:

“(Muna) nan a ofishin ‘yan sanda har yanzu. Na kasance a casun 4/20 a Asokoro amma suka tashe shi. Asokoro, Abuja. Akwai daruruwan mu a tsare a yanzu. Ina tsammanin ya zuwa yanzu an gama lissafa kowa."

Kara karanta wannan

Harin Bam a gidan giya a Taraba: Kawo yanzu mutum 16 sun mutu

Sai dai, Legit.ng Hausa ta bi diddigin bayanan asusun @Ezioimmauel a shafin na Twitter bata samu ba, alamar da ke ko dai an goge asusun ko kuma babu shi.

A bangare guda, Babafemi ya tabbatar da kame da cewa:

“Mun damke wasu matasa da ke wani bikin casun tabar wiwi a Abuja. Baya ga casun akwai bikin kaddamar da sabon abin sha. Mata uku ne suka shirya taron. Suna hannunmu. Za mu fitar da sanarwa kan lamarin nan ba da jimawa ba.”

Jim kadan Legit.ng Hausa ta bi shafin Twitter na NDLEA, inda ta ga sanarwar da ke bayyana cewa, akalla mutane 200 ne aka kama, kuma yanzu haka an dauki bayanansu.

Tonon silili: Bayan shiga hannu, barawo ya nuna sirrin yadda yake shiga gida ta taga

A wani labarin, wani da ake zargin barawo ne ya nuna abin da da yawan masu amfani da shafin Instagram suka kira "tsagwaron hazaka" lokacin da aka gan shi yana shiga wani gida ta wata karamar taga.

Kara karanta wannan

Shari'a a Najeriya: An yankewa Barawon Manja hukuncin shekaru 6 a Magarkama

An tilasta wa barawon ya nuna yadda ya shiga wani gini ta taga wanda aka kwatanta girmansa da ramin tattabara.

Ga mamakin wadanda suke wurin, sai kawai suka ga mutumin ya shiga gidan yana ta rarrafe kamar maciji yana ratsawa kamar dai jarumin fim din Spider-Man.

Asali: Legit.ng

Online view pixel