IPOB ta saki jerin sunayen yan bindigar da ke kashe-kashen mutane a kudu maso gabas

IPOB ta saki jerin sunayen yan bindigar da ke kashe-kashen mutane a kudu maso gabas

  • Lamarin rashin tsaro na ci gaba da ta'azzara a yankin kudu maso gabashin kasar musamman ma a jihar Imo
  • Sai dai kuma a yayin da ake yawan zarginta da kai hare-hare, kungiyar IPOB ta fito ta magantu inda ta daura laifin kashe-kashen da ake fama da shi kan tawagar tsaro na Ebubeagu
  • A takaice dai kungiyar masu neman kafa kasar Biyafaran ta lissafo sunayen wasu mutane da ta ce sune ke haifar da karya doka a yankin da ake magana a kai

Imo - Yayin da yankin kudu maso gabashin kasar ke ci gaba da fuskantar kashe-kashen mutane da sauran ayyukan ta’addanci, kungiyar aware ta masu neman kafa kasar Biyafara ta daura laifin kan wasu tawagar yan tsaro na Ebubeagu.

Kungiyar ta yi zargin cewa mambobin kungiyar tsaron Ebubeagu ne ke da alhakin kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba a jihar Imo da kudu maso gabashin kasar.

Kara karanta wannan

‘Yan Boko Haram sun sake sace mata a garin Chibok bayan sun kashe ‘Dan banga

IPOB ta saki jerin sunayen yan bindigar da ke kashe-kashen mutane a kudu maso gabas
IPOB ta saki jerin sunayen yan bindigar da ke kashe-kashen mutane a kudu maso gabas Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Kungiyar ta kuma lissafo sunayen shugabannin da ke aiwatar da kashe-kashen mutanen a yankin Orlu na jihar Imo a matsayin:

1. Chibuike Igwe

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

2. Paul Udenwa daga Amaifeke Orlu

3. Okwudili Dim wanda aka fi sani da ‘One Nigeria’

4. Mutumin da ake kira Sky daga Umutanze Orlu

5. Mutumin da ake kira 2men daga Umuna a Orlu.

Sauran mutanen da ke addaban yankin sune:

1. Cyril Amasiatu wanda aka fi sani da wasara

2. Iron Agbaradu daga Amagu

3. Chinedu kwamandan Agbaradu-Amagu

4. Cheta odinkenma – Amagu

5. Uchenna Nwachukwu

6. Chibyke Gezek Amagu

7. Chukwudi Odimegwu

Masu yiwa mambobin ESN sojan gona a Orsu Ihiteukwa Uru

1. Mutumin da ake kira Sky

2. Mutumin da ake kira “No one”

Kara karanta wannan

2023: Deleget na Jihohi 10 da Tinubu ke bukata don lashe zaben fidda gwanin APC

3. Mutumin da ake kira “Double lion”

4. Mutumin da ake kira “Commander”.

A cewar kungiyar, wadannan mutane da aka ambata a sama sune ke aikata kashe-kashen mutane a yankin.

“Wadannan mutanen da aka ambata a sama suna da hannu a wajen aikata laifukan da ke faruwa a wadannan garuruwa da suka hada da garkuwa da mutane, sace-sacen motoci da sauransu. Don haka kungiyar IPOB ta ayyana nemansu ruwa a jallo, kuma duk wanda ya bayar da bayanai masu amfani zai samu tukwici mai tsoka.
“Wadannan miyagu da aka ambata a sama sun yiwa mutanenmu da ke zama a yankin Orlu na jihar Imo barna sosai. A kodayaushe IPOB na fada ma jama’a cewa wadannan yan iska da aka ambata a sama suna daga cikin laifukan da ke faruwa a kasarmu.
“Kada a bari wani bara-gurbi ya bata IPOB. Ya kamata a hukunta wadannan shaidanun da masu daukar nauyinsu.”

Kara karanta wannan

Al-mundahana: EFCC ta Tsare Ɗan Tsohon Gwamnan Nasarawa kan wasu Kudade N130m

Wasu yaan siyasa na bayan kashe-kashen yan bindiga, Gwamnan APC ya faɗi wani sirri bayan ganawa da Buhari

A wani labari, gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, jiya Talata ya roki yan siyasan ƙasar nan su yi siyasa ba tare da ƙiyayya ba kuma su dakatar da zubar da jinin mutane yayin da suke neman ɗarewa madafun iko.

Ya yi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da manema labaran gidan gwamnati jim kaɗan bayan gana wa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.

Gwamnan ya kuma musanta zargin cewa gwamnati ce ke ɗaukar nauyin ayyukan yan bindiga, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel