Wasu yan siyasa na bayan kashe-kashen yan bindiga, Gwamnan APC ya faɗi wani sirri bayan ganawa da Buhari
- Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo ya ce yanzun ba shi da wata tantama kan mutanen dake ɗaukar nauyin 'yan bindiga
- Bayan gana wa da shugaba Buhari a Aso Villa, Uzodinma ya roki yan siyasa su daina siyasa da gaba, su yi siyasa da tsafta
- Ya ce zuwa yanzun yan sanda sun kama mutum 2 kuma suna ba da haɗin kai wajen tono abinda ke kewaye da kisan ma'aikacin INEC
Abuja - Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma, jiya Talata ya roki yan siyasan ƙasar nan su yi siyasa ba tare da ƙiyayya ba kuma su dakatar da zubar da jinin mutane yayin da suke neman ɗarewa madafun iko.
Ya yi wannan furucin ne yayin da yake zantawa da manema labaran gidan gwamnati jim kaɗan bayan gana wa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari.
Gwamnan ya kuma musanta zargin cewa gwamnati ce ke ɗaukar nauyin ayyukan yan bindiga, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
Ya kuma yi mamakin ta ya gwamnonin jihohin Imo, Kaduna da Ebonyi za su yi farin ciki da salwantar da rayuka da dukiyoyi, idan har zargin da ake gaskiya ne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Uzodinma ya ce:
"Na daina tantama kan mutanen dake ɗaukar nauyin yan bindiga a Najeriya. Waɗan da ke son tarwatsa Najeriya ta koma ba shugabanci, ba zai yuwu ace su ke kan madafun iko ba."
"Duk bayan haka, ba wannan shekaran da muke ciki za'ayi zaɓe ba, sai shekara mai kamawa za'a fara hada-hadar zaɓe."
"Ya kamata mu fifita Najeriya, ƙasar mu ta zama abu na farko da ya fi komai a cikin zuciyarmu."
Ina aka kwana kan kisan ma'aikacin INEC?
Gwamnan ya ce zuwa yanzun an kama yan bindiga biyu bayan kashe ma'aikacin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa.
A cewarsa, suna baiwa jami'an tsaro haɗin kai wajen binciken da ake domin gano musabbabi da kuma waɗan da ke da hannu a kisan jami'in INEC a wurin rijistar zaɓe.
A wani labarin na daban kuma Bayan biyan kuɗin fansa, Malamin Jami'a da yan bindiga suka sako ya rasu
Awanni bayan kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane wani Malamin Jami'a ya rasu a kan hanyar zuwa Asibiti.
Lakcaran mai suna, Farfesa Ovaborhene Idamoyibo, ya shiga hannun yan ta'adda ne ranar 9 ga watan Afrilu, suka sako shi ranar Lahadi.
Asali: Legit.ng