‘Yan Boko Haram sun sake sace mata a garin Chibok bayan sun kashe ‘Dan banga

‘Yan Boko Haram sun sake sace mata a garin Chibok bayan sun kashe ‘Dan banga

  • Mayakan kungiyar Islamic State West Africa Province sun kai wani hari a kudancin jihar Borno
  • ‘Yan ta’addan da aka fi sani da ISWAP sun kashe ‘dan banga, sun dauke yara akalla shida a Chibok
  • Wata majiya ta bayyana cewa yara kusan hudu da aka yi gaba da su, sun fito ne daga gida daya

Borno - A lokacin da ake bakin cikin cika shekara takwas da Boko Haram suka sace ‘yan makaranta a Chibok, ‘yan ta’addan sun sake yin wata barnar.

Jaridar Daily Trust ta ce sojojin Islamic State West Africa Province sun dawo garin Chibok da ke jihar Borno a kwanan nan, sun kuma dauke wasu ‘yan mata.

A makon da ya wuce mutanen garin na Chibok suka shirya addu’a na musamman a harabar makarantar GGSS Chibok domin tuna abin da ya faru a 2014.

Kara karanta wannan

Jirgin Super Tucano ya yi wa ISIS lahani, ya kashe ‘Dan ta’addan da ake takama da shi

A ranar Lahadi aka samu labarin ‘yan ta’addan sun kuma hallaka wani matashi da yake aikin banga na sa-kai domin tsare dukiya da rayukan Bayin Allah.

Kamar yadda rahoton ya bayyana, wannan ‘dan banga mai suna Godwin ya mutu yana shekara 17.

An shiga Yimir Mugza

‘Yan ta’addan na kungiyar ISWAP sun zo a kan babura da kananan motoci da-dama, suka dura kauyen Yimir Mugza, su ka shiga budawa jama'a wuta.

‘Yan Boko Haram
Tunawa da 'Yan makarantar Chibok Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Jaridar ta ce hakan ta sa dole mutanen kauyen suka rika ficewa daga gidajensu, su na shiga daji.

Baya ga Godwin da aka kashe, ana zargin ‘yan ta’adan sun sace abinci, babura, da abin hawa. Haka zalika mayakan na ISWAP sun yi gaba da dabbobi.

Hari na bakwai tun 2014

Wani jami’in tsaro ya shaidawa jaridar cewa wannan hari da aka kawo shi ne na bakwai da mutanen garin Chibok suka gani daga 2014 zuwa yanzu.

Kara karanta wannan

Luguden wuta: Sojojin Najeriya sun ragargaji yan bindiga, sun tura da yawa lahira a jihar Arewa

Majiyar ta ce an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin tabbatar da abubuwa sun dawo daidai. An hangi dakarun sojoji sun bayyana a halin yanzu a kauyen.

‘Yan mata hudu daga cikin yaran da aka dauka a wannan harin, duk sun fito ne daga dangi daya.

Ba yau aka fara ba

A Junairun 2022 aka ji labari cewa mayakan Boko Haram sun sake garkuwa da 'yan mata a Chibok bayan sun kona gidaje sama da 100 a wani mugun hari.

A watan Afrilun 2014 ne wannan gari da ke kudancin Borno ya gamu da tashin hankali. ‘Yan ta’adda suka dauke yara 276 masu rubuta jarrabawar WAEC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel