2023: Deleget na Jihohi 10 da Tinubu ke bukata don lashe zaben fidda gwanin APC

2023: Deleget na Jihohi 10 da Tinubu ke bukata don lashe zaben fidda gwanin APC

Mutane sun bayyana mabanbanta ra'ayi bisa niyyar tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu,na zama shugaban kasa a 2023.

Yayinda wasu suka bayyana goyon bayansa a fili, wasu sunce ya tsufa da yawa, ba zasu zabesa ba.

A wannan rahoto, Legit.ng ta tattaro muku jihohi 10 masu muhimmanci da Tinubu ke bukata don lashe zaben fidda gwani karkashin jam'iyyar APC.

Tinubu Osinbajo
2023: Deleget na Jihohi 10 da Tinubu ke bukata don lashe zaben fidda gwanin APC Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga jerin jihohin da zamu yi magana kansu:

1. Kano

2. Katsina

3. Borno

4. Osun

5. Lagos

6. Oyo

7. Jigawa

8. Niger

9. Ogun

10. Nasarawa.

1 Kano:

Kara karanta wannan

IPOB ta saki jerin sunayen yan bindigar da ke kashe-kashen mutane a kudu maso gabas

Ganduje da Shekarau ne iyayen siyasar APC a jihar Kano. duk da sabanin dake tsakaninsu, Ganduje da Shekarau magoya bayan Tinubu ne kuma zasu goya masa baya.

Hakazalika Shugaban kwamitin kungiyoyin magoya bayan Tinubu, Abdul Mumini Jibrin, dan jihar Kano ne.

Kano na da deleget 465.

2 Katsina.

Gwamna Aminu Bello Masari na daga cikin magoya bayan Tinubu. Ana kyautata zaton cewa Tinubu zai lashe zaben fidda gwanin APC.

Katsina na da deleget 384.

3 Borno

Kashim Shettima, tsohon gwamnan jihar Borno kuma mai gidan Gwamnan Borno mai ci yanzu, Babagana Umara Zulum, na daga cikin manyan makusantan Tinubu kuma masu yi masa yaki dare da rana.

4 Osun

Ko shakka babu, deleget 308 na jihar Osun yan gidan Tinubu ne. Tinubu ne babban mai gidan gwamnan jihar.

5 Lagos

Babu bukatar bata lokaci, Tinubu wanda shine uban siyasan Legas zai lashe kuri'un deleget 304.

6 Oyo

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Tsaffin Gwamnoni da Gwamnoni masu ci ke raba kan 'ya'yan jam'iyya, Abdullahi Adamu

Duk da kasancewar manyan jiga-jigan APC a jihar na komawa PDP, Tinubu na iya samun kashi 70% na kuri'un deleget na Oyo 292

7 Jigawa state.

Gwamnan Jigawa babban na hannun daman Tinubu ne, hakazalika tsohon gwamnan jihar Saminu Turaki.

Jigawa dake da deleget 266. Tinubu na bukatarsu

8 Niger:

A yayinda Tinubu ya kai ziyara jihar Neja, gwamna Abubakar Sani Bello da kansa ya bayyana goyon bayansa garesa.

9 Ogun:

Nan rikicin take: Kasancewa Osinbajo dan asalin jihar Ogun, shin gwamnan jihar Dapo Abiodun zai yi watsi da dan jiharsa ya goyi bayan Tinubu wanda ya taimaka masa ya zama gwamna?

Ogun na da deleget 248.

10 Nasarawa

Gwamna Abdullahi A. Sule wata rana ya sanya hular Tinubu a taron majalisar zartaswar jiharsa. Babban magoyi bayansa ne.

Nasarawa na da deleget 245.

Asali: Legit.ng

Online view pixel