Shirin 2023: Yanzu dai 'yan Najeriya sun fahimci PDP ce gatansu, in ji Sule Lamido

Shirin 2023: Yanzu dai 'yan Najeriya sun fahimci PDP ce gatansu, in ji Sule Lamido

  • Jigon jam'iyyar PDP, Sule Lamido ya bayyana yadda PDP ke shirin kawo ci gaba a Najeriya a 2023
  • Ya bayyana haka ne a shirin gidan talabijin, inda yace PDP ce makoma mai kyau ga 'yan Najeriya a yanzu
  • Tsohon gwamnan na jihar Jigawa ya ce, sam Najeriya ta daidaice a yanzu, akwai bukatar dawo da hadin kai

Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, ya ce a yanzu da 'yan Najeriya na kallon jam'iyyar PDP a matsayin fata daya tilo a garesu, TheCable ta tattaro.

Da yake magana yayin wani shiri a gidan Talabijin na Channels, a ranar Lahadi, tsohon gwamnan ya ce shirye-shiryen da jam’iyyar ke ci gaba da yi dangane da babban zaben 2023 na ganin amfani da ci gaban kasa ne.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ga ASUU: Ku yi hakuri ku koma aji ku ci gaba da karantarwa

Ya ce neman goyon baya da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP ke yi a fadin kasar nan zai kara daukaka martabar jam’iyyar.

Sule Lamido kan faduwar PDP a zaben 2015
Shirin 2023: Yanzu dai 'yan Najeriya sun fahimci PDP ce gatansu, in ji Sule Lamido | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

A cewarsa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A PDP, duk abin da za mu yi don amfanin Najeriya shi muke yi, ba na mu ba. Jama’a na ganin PDP ce kawai fata a Najeriya a yau.
“Muna duba abin da muka fito da shi kuma ‘yan Najeriya za su ji dadin hakan kuma za su ba su yanayin da zai dawo da kaunar juna da aminci tsakanin juna.
“A gare ni, kafin ku yi wani abu, muna bukatar mu maido da amana a tsakaninmu.
“A bayyane yake, a Najeriya a yau, ba mu amince da juna ba. Ba mu jin yarda da junanmu yanzu. Hadin gwiwarmu babu ita a yanzu. Dangantakarmu daya ita ce dan adamtaka."

Kara karanta wannan

Farawa da iyawa: Takarar Shugaban kasar da Ngige zai yi a 2023 ta gamu da bakin jini

'Yan Najeriya suka fadi a 2015, ba PDP ba

Hakazalika, Sule Lamido ya tuno zaben 2015, inda yace 'yan Najeriya suka fadi ba wai jam'iyyar PDP ba.

Ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan yadda Najeriya ta zama a hannun 'yan siyasar jam'iyyar APC, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Ya ce:

“Akwai wata jam’iyya mai suna PDP da ta ci zabe a 1999, 2003, 2007, 2011 amma ta fadi a 2015. Don haka ‘yan Najeriya ne suka san PDP sosai.
"Ba mu fadi zabe ba a 2015 ko 2019, ’yan Najeriya ne suka fadi a zabe; ‘Yan Najeriya ne suka yi asara ba mu ba.”

Bai dace kuna Instagram ba amma baku da katin zabe, Tinubu ga matasa

A wani labarin, Bola Tinubu, dan takarar shugabancin kasa karkashin jam'iyyar APC mai fatan gaje kujerar shugaba Buhari, ya ce bai kamata matasa su cigaba da kokawa ba,

Kara karanta wannan

2023: Abu ɗaya zai kawo karshen yan bindiga a Najeriya, Gwamnan dake son gaje Buhari ya gano

The Cable ta ruwaito. Tsohon gwamnan Legas din ya shawarci matasa da su yi aiki tukuru wajen ganin sun gina sabuwar kasar da zata samar da dama da cigaba mara iyaka.

Tinubu ya ce bai kamata matasa su cigaba da ziyartar kafafan sada zumuntar zamani irinsu Instagram ba, bayan basa da katikan zaben da zasu zabi shugabannin da suke so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel