Abin da Buhari ya fadawa masu neman kujerar shi a APC da su ka hadu a fadar Aso Villa

Abin da Buhari ya fadawa masu neman kujerar shi a APC da su ka hadu a fadar Aso Villa

  • Wadanda su ke sha’awar yin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC sun dage wajen samun tikiti
  • A dalilin wannan ne Bola Tinubu, David Umahi da Kayode Fayemi su ka zauna da shugaban kasa
  • Muhammadu Buhari bai fadawa kowa ya janye takararsa ba, kuma bai ce zai mara masa baya ba

Abuja - Masu neman takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC mai mulki sun yi zama da Muhammadu Buhari kafin sanar da Duniya aniyarsu.

Jaridar Punch ta fahimci cewa Mai girma shugaban kasar ya fadawa masu shirin yin takarar cewa su je su tallata kansu ga al’ummar da za su kada kuri’a.

Wata majiya a fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa Muhammadu Buhari bai nemi ko daya daga cikin masu takara ya janye burin da yake da shi ba.

Kara karanta wannan

Ka yi abin kirki: Gwamnan PDP ya yabi Buhari kan yafewa Joshua Dariye da Jolly Nyame

Abin da Buhari ya fada masu shi ne, ka da su bata sunan jam’iyyar APC da kuma gwamnatin da ya ke jagoranta a yayin da suke kokarin yakin neman zabe.

Kawo yanzu, Legit.ng Hausa ta na da labari shugaba Buhari ya zauna da Asiwaju Bola Tinubu, David Umahi da Kayode Fayemi duk kan batun takara a APC.

A duk haduwar da shugaban Najeriyan yake yi da wadanda su ke da kudiri burin zama magadansa, bai nunawa wani zai fito ya mara masa baya ba.

Buhari a fadar Aso Villa
Muhammadu Buhari a taro Hoto: @bashahmad
Asali: Facebook

Rahoton ya ce sannan kuma babu wanda zai iya cewa Buhari ya fada masa ya hakura da neman mulki.

Baya ga haka, Mai girma shugaban kasar ya bukaci jin irin manufofin da suka zo da shi, tare da tabbatar da cewa su na goyon bayan kadarorin gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

Dattawan Arewa na jin haushin Buhari ne don ya hanasu mukamai a gwamnatinsa: Fadar Shugaban kasa

Bincike a game da abin da ‘ya ‘yan APC suke zuwa gaban Muhammadu Buhari da shi, majiyat ta ce wasu su na neman albarkarsa ne ba izinin yin takara ba.

Ana tunani mutum daya ne ya nemi izinin shugaba Buhari da ya ba shi damar ya fito takara. Zuwa yanzu ba a san wanene wannan cikin masu harin ba.

Buhari ya bar mutane a duhu

Daily Trust ta ce rashin sanin inda Buhari ya dosa ya na daburta lissafin ‘yan jam’iyyarsa. A dalilin haka, wasu ‘yan takara su ka jinkirta fito da aniyar ta su.

Irinsu Dr. Kayode Fayemi sun fara abin da ake ganin fadanci ne domin samun tikiti. Shi kuma Yemi Osinbajo ya yi alkawarin cigaba daga inda Buhari ya tsaya.

Tinubu ya huro wuta

Kwanaki aka ji labari shugabannin majalisun dokoki na jihohin kasar nan da ke karkashin jam’iyyar APC mai mulki sun yi zama da Bola Tinubu a garin Legas.

Kara karanta wannan

'Yan Daba Sun Jefi Alkali Da Ɗuwatsu Yayin Zaman Kotu, An Fice Da Shi Ba Shiri

Asiwaju Tinubu ya na neman goyon bayan ‘ya ‘yan APC, kuma sun yi masa alkawarin za su mara masa baya, har ya yi nasarar samun takarar shugaban kasa a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel