Tinubu Ya Kai Wa El-Rufai Ziyara, Ya Gwangwaje Wadanda Harin Jirgin Kasan Kaduna Ya Ritsa Da Su Da N50m

Tinubu Ya Kai Wa El-Rufai Ziyara, Ya Gwangwaje Wadanda Harin Jirgin Kasan Kaduna Ya Ritsa Da Su Da N50m

  • Tsohon Gwamnan Jihar Legas, Bola Tinubu ya isa Jihar Kaduna don ganawa da Gwamna Nasir El-Rufai da kuma jaje ga mutanen jihar
  • Ya je ne tare da tsohon gwamna Jihar Borno, Kashim Shettima a ranar Talata musamman akan farmakin da ‘yan bindiga suka kai wa jirgin kasa wanda suka tafka barna
  • Gwamnan ya tarbi tawagar tasu tare da Sanata Uba Sani da Sanata Abdu-Kwari a Sir Kashim Ibrahim House inda Tinubu ya gwangwaje wadanda aka kai wa harin da N50m

Kaduna - A ranar Talata tsohon Gwamnan Jihar Legas ya kai ziyara Kaduna don jajanta wa Gwamna Nasir El-Rufai da mutanen jiharsa akan harin da ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin kasa, Channels TV ta ruwaito.

Tinubu ya samu rakiyar tsohon Gwamnan Jihar Borno, Sanata Kashin Shettima, wanda ya sanar da batun bayar da kyautar N50m ga wadanda harin jirgin kasan ya ritsa da su.

Kara karanta wannan

2023: Wike ya jagoranci gwamnonin PDP zuwa wajen Janar Babangida da Abdussalami

Tinubu Ya Kai Wa El-Rufai Ziyara, Ya Gwangwaje Wadanda Harin Jirgin Kasan Kaduna Ya Ritsa Da Su Da N50m
Tinubu Ya Ziyarci El-Rufai, Ya Gwangwaje Wadanda Harin Jirgin Kasan Kaduna Ya Ritsa Da Su Da N50m. Hoto: @GovKaduna
Asali: UGC

Gwamna El-Rufai, Sanata Uba Sani da Sanata Abdu-Kwari sun amshe su a Sir Kashim Ibrahim House.

Tinubu ya samu rakiyar wasu manyan mutane

Sauran wadanda suka biyo tawagar Tinubu bisa ruwayar Channels TV sun hada da tsohon kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara da Sanata Abu Ibrahim.

Tinubu ya kwatanta harin a matsayin babbar masifa.

A cewarsa kowa ya shiga damuwa duba irin hare-haren da ake kaiwa Jihar Kaduna wanda ya ke janyo halakar daruruwan rayuka da dukiyoyi.

Ya kara da cewa ya kamata a kawo karshen kashe-kashen da ake yi a jihar.

Tinubu ya roki Gwamnan El-Rufai da ya kwantar da hankalinsa ya ci gaba da dagewa wurin yin shugabanci na kwarai.

El-Rufai ya mika godiyarsa ga Tinubu

Ya kara da rokon mutanen Najeriya da su bai wa gwamnatin Jihar Kaduna hadin kai wurin kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga.

Kara karanta wannan

Ramadan: Bola Tinubu ya yi kira na musamman ga al’ummar Musulmi a kan watan azumi

A bangaren Gwamna El-Rufai ya yi godiya ga Tinubu akan nuna wa mutanen Jihar Kaduna soyayya ta hanyar kin yin shagalin cikarsa shekaru 70 saboda wadanda aka kashe a harin jirgin kasa.

El-Rufai ya ce yana sane da burin Tinubu na zama shugaban kasa inda ya kara da cewa yanzu haka Najeriya tana mawuyacin hali don haka sai ya daura dammarar yin aiki tukuru don zama shugaba nagari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel