2023: Wike ya jagoranci gwamnonin PDP zuwa wajen Janar Babangida da Abdussalami

2023: Wike ya jagoranci gwamnonin PDP zuwa wajen Janar Babangida da Abdussalami

  • Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da wasu gwamnoni sun kai ziyara wajen Abdussalami Abubakar
  • Shi kuma Janar Abdussalami Abubakar ya kai ‘yan siyasar gaban tsohon shugaba, Ibrahim Babangida
  • Akwai gwamnoni hudu, Kashim Imam, Sanata Suleiman Nazifi da wani tsohon Sanatan jihar Ribas

Niger - Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike ya kai ziyara zuwa jihar Neja a kokarin da yake yi na tuntubar mutane game da batun neman mulki a 2023.

Punch ta ce Gwamna Nyesom Wike ya yi zaman musamman da Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Janar Abdussalami Abubakar a garin Minna.

Wadanda suka yi wa Gwamnan rakiya sun hada da abokan aikinsa na jihohin Abia, Enugu da Oyo; Okezie Ikpeazu, Ifeanyi Ugwuanyi da Seyi Makinde.

Tawagar ta sa labule da manyan kasar ne na kusan kimanin sa’a guda. Har zuwa yanzu, Legit.ng Hausa ba ta da ainihin masaniyar kus-kus din da aka yi.

Kara karanta wannan

2023: Tambuwal da Peter Obi za su shiga labule da masu ruwa da tsaki na PDP a majalisar tarayya a yau

Sai dai ana zargin cewa taron bai rasa nasaba da neman shugabancin da Wike ya ke yi a PDP, kuma yana ganin ya kamata mulki ya koma kudu ne a 2023.

2023: Wike a Minna
Nyesom Wike tare da Abdussalami Abubakar da Ibrahim Babangida Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abin da ya kawo mu Neja - Okezie Ikpeazu

Bayan taron, gwamnan jihar Abia, Okezie Ikpeazu ya shaidawa manema labarai cewa sun zo garin Minna ne domin su yi magana da tsohon shugaban.

“Na zo ne tare da abokan aiki na, gwamnonin Enugu, Oyo, Ribas da ‘yan majalisar tarayyar domin mu tuntubi tsohon shugaban kasa a kan matsalolin kasar nan.”

- Okezie Ikpeazu

Ikpeazu ya ce makasudin zuwa wajen Abdussalami Abubakar shi ne a tattauna a kan halin tsaro da tattalin arzikin da kasa ta ke ciki, tare da yabawa kokarinsa.

Jaridar PM News ta ce bayan zama da Janar Abdulsalami, ya jagoraci ‘yan siyasar zuwa wajen Babangida, wanda ya ke burin wani mai jini a jika ya karbi mulki.

Kara karanta wannan

Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaro, billahi lazi zamu dauko Sojin haya: El-Rufa'i ya fusata

Wike su na tare da manyan 'yan siyasa

Rahoton ya ce tsohon gwamnan jihar Benuwai, Gabriel Suswam ya na cikin wannan tawaga da ta gana da tsofaffin shugaban kasar a ranar Litinin a babban brinin Neja.

Sauran ‘yan tafiyar sun hada da Kasim Imam, Sanata Suleiman Nazifi da wani tsohon Sanatan Ribas.

An raba kawun 'Yan PDP

Kun samu rahoto dazu cewa kan wadanda ke neman tikitin takarar shugaban kasa a PDP ya rabu uku tsakanin Atiku Abubakar, Nyesom Wike da su Bukola Saraki.

An samu bangarori uku da suke da mabanbantan ra’ayi a game da yankin da za a kai takara. Wike da mutanensa su na ganin 'Yan kudu ya kamata su yi mulki yanzu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel