Ramadan: Bola Tinubu ya yi kira na musamman ga al’ummar Musulmi a kan watan azumi

Ramadan: Bola Tinubu ya yi kira na musamman ga al’ummar Musulmi a kan watan azumi

  • Jagoran jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, ya fitar da jawabi na musamman a kan watan Ramadan
  • Bola Tinubu ya taya duk Musulman da ke Duniya farin cikin shigowar wannan watan mai alfarma
  • ‘Dan siyasar ya yi kira ga mutane su dage da addu’o’i tare da kuma taimakawa masu karamin karfi

Lagos - Daya daga cikin jagororin siyasar Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu ya yi magana a yayin da duk Musulmai su ka soma azumin watan Ramadan.

Legit.ng ta samu labari cewa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya taya daukacin Musulman Najeriya da sauran kasashen Duniya shigowa wata mai alfarma.

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bayyana haka ne a wani jawabi na musamman da ya fitar ta bakin babban hadiminsa, Tunde Rahman a makon nan.

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

A jawabin na sa, Bola Tinubu ya yi kira ga jama’a da su nuna soyayya, da kauna da fahimtar juna.

Mu sa Najeriya a addu'a - Bola Tinubu

‘Dan siyasar ya yi kira na musamman ga Musulman da ke azumi da su ribaci wannan wata mai daraja wajen yi wa Najeriya addu’a a halin da ake ciki.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Tinubu ya bada shawarar a bazama wajen sa kasar nan a addu’a ganin kalubalen da ake fuskanta. A ‘yan kwanakin nan ana fama da matsalolin rashin tsaro.

Bola Tinubu
Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a filin idi Hoto: punchng.com
Asali: UGC

An rahoto mai neman kujerar shugaban kasar ya na mai kira ga Bayin Allah su taimakawa na-kusa da su da suke cikin bukata a lokacin watan na Ramadan.

A cewar Tinubu, Ubangiji ya albarkaci Najeriya, amma wasu ‘yan tsiraru su na tada kafar baya.

Bangaren jawabin Tinubu

“Da wannan sakon, ina taya ‘yanuwa Musulmai a Najeriya da fadin Duniya a game da shigowar watan Ramadan mai daraja da kuma fara azumi.”

Kara karanta wannan

Ana maganar rufe Majalisa domin tursasa Shugaban kasa ya tashi-tsaye kan lamarin tsaro

“Wannan ne watan Musulunci da ake yin azumi. Ramadan lokaci ne mai daraja kuma na musamman.”
“Ramadan ya na koya mana riko da halaye kwarai, kaunar makwabtanmu, da kuma taimakawa talakawa, marasa karfi da gajiyayyu a cikinmu.”

- Bola Tinubu

Buhari ya saurari Tafsir

A jiya aka ga wasu hotunan Shugaban Kasar Najeriya Muhammadu Buhari da hadiman sa suka fitar lokacin da ya ke sauraron tafsirin Al-qur'ani mai girma.

Muhammadu Buhari ya je wajen karatun tafsirin a fadarsa da ke garin Abuja. Musulamai su kan yi amfani da watan azumi domin yin darasin littafi mai tsarki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel