Yadda NRC ta yi watsi da gargadin da aka yi mata kan shirin kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

Yadda NRC ta yi watsi da gargadin da aka yi mata kan shirin kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna

  • NRC ta yi karin haske kan kokarin da aka dinga kan dakile farmakin da 'yan ta'adda suka kai wa jirgin kasa fasinjoji na Abuja zuwa Kaduna
  • Kamar yadda majiya mai tushe ta sanar, hukumomin tsaro sun shawarci NRC da ta soke tashin jiragen dare amma ta yi kunnen uwar shegu da hakan
  • Shugaban ma'aikatan tsaro ya bada umarnin a kawar da 'yan ta'adda kafin su kai farmakin tunda an samu rahotannin sirri kafin ranar

Hukumar kula da ayyukan jirgin kasan Kaduna sun yi karin haske kan gazawar jami’ai a matakai daban-daban wajen dakile farmakin da aka kai wa jirgin kasa, wanda aka samu gargadi tun watanni da suka gabata.

Wasikun da aka aike wa hukumomin tsaro da Daily Trust ta gani sun bayyana yadda aka bankado wannan makarkashiyar biyo bayan kutsen da jami’an leken asiri suka yi wanda ya kai ga fitar da sanarwar ga hukumomi daban-daban.

Kara karanta wannan

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

Yadda NRC ta yi watsi da gargadin da aka yi mata kan shirin kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna
Yadda NRC ta yi watsi da gargadin da aka yi mata kan shirin kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Manyan jami’an tsaro na zargin jami’an hukumar kula da sufurin jiragen kasa ta Najeriya NRC da kin bin shawarar da aka ba su na takaita zirga-zirgar jiragen kasa zuwa rana kadai banda dare.

Bayanai na baya-bayan nan sun tabbatar da labarin da jaridar Daily Trust ta buga a ranar Alhamis din da ta gabata, wanda ke bayyana cewa harin bam din da aka kai wa jirgin fasinjojin hari da shi duk an san da za a saka shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Harin da aka kai kan jirgin, wanda ya ritsa da fasinjoji sama da 300, ya kasance mafi muni da ya faru bayan a kalla sau uku a baya an yi yunƙurin amma ba a samu nasara ba.

A kalla gawarwaki tara ne aka zakulo daga wurin da aka kai harin a ranar Litinin yayin da wasu 26 suka samu raunuka. Masu garkuwa da mutanen sun yi awon gaba da wasu fasinjojin da har yanzu ba a tantance yawansu ba.

Kara karanta wannan

Shehu Sani: Lokaci ya yi da ya kamata a bar 'yan Najeriya su mallaki makami

Bangarorin biyu na gargadin tsaro sun mayar da hankali ne kan umarnin kafaike sojoji a yankin don mayar da martani ga barazanar da kuma NRC ta dakatar da tafiye-tafiyen dare a kan hanyar.

Rundunar ‘yan sandan Najeriya karkashin sashin kula da harkokin tsaron cikin gida ta kan tura ‘yan sanda dauke da makamai a cikin jirgin domin tabbatar da tsaro.

Sai dai kamar yadda wasu jihohi da dama ke fama da kalubalen tsaro da yayi muni, jihar Kaduna na da rundunonin sojoji da ke karkashin mabambantan ma’aikatun da ke karbar kula da tsaro a jihar.

Sai dai, a takardun da Daily Trust ta gani da kuma bayanai daga majiya mai tushe, sun nuna cewa bayan shawarwari guda uku daban-daban da gargadi, a kalla an yi taro biyu na dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa da maraice amma NRC ta yi kunnen uwar shegu da hakan.

Hakazalika, rundunonin soji a yankin sun kasa daukar matakin dakile harin da aka dinga shirin kai wa.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye da bayanan mutanen da suka mutu a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Manyan kwamandojin soji sun ba da takamaiman umarni ga sojoji kan su far wa maboyar masu laifi'yan ta'addan da sauran wuraren da za a iya amfani da su gabanin harin.

Obi na Onitsha: Amsa waya ya hana ni hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa farmaki

A wani labari na daban, Mai martaba Sarkin Onitsha na Jihar Anambra, Mai Martaba Igwe Nnaemeka Alfred Ugochukwu Achebe, ya bayyana yadda ya kubuta daga hawan jirgin Abuja zuwa Kaduna da ‘yan ta’adda suka kai wa farmaki a ranar Litinin, 28 ga watan Maris.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Sarkin zai hau jirgin amma kiran wayar da aka yi masa na wasu mintina yasa ya rasa hawan jirgin.

A wannan rana mai muni ne ‘yan ta’adda suka kai farmaki kan jirgin kasan da ya taho Kaduna. Sun jefa bama-bamai a kan layin dogo, lamarin da ya tilasta wa jirgin tsayawa, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ga 'yan Najeriya: Ku tarawa 'yan uwanku talakawa da harin jirgi ya shafa kudin magani

Asali: Legit.ng

Online view pixel