Shehu Sani: Lokaci ya yi da ya kamata a bar 'yan Najeriya su mallaki makami

Shehu Sani: Lokaci ya yi da ya kamata a bar 'yan Najeriya su mallaki makami

  • Sanata Shehu Sani ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta baiwa yan Najeriya yancin mallakar makami
  • Tsohon dan majalisar dokokin kasar na martani ne kan hare-haren baya-bayan nan da yan bindiga suka kai kan jiragen kasar wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka
  • Sani ya ce idan aka baiwa yan kasar damar daukar makami a nan ne za a gane wanda ke da kasar

Kaduna - Tsohon dan majalisar dokokin kasar wanda ya wakilci yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa, Sanata Shehu Sani, ya magantu a kan lamarin rashin tsaro.

Shehu Sani ya ce duba ga yadda lamarin tsaro ke kara tabarbarewa a kasar, ya kamata a bari yan Najeriya su dunga daukar makamai domin kare kansu a hukumance.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ga 'yan Najeriya: Ku tarawa 'yan uwanku talakawa da harin jirgi ya shafa kudin magani

Legit Hausa ta rahoto yadda yan bindiga suka kai harin bam a kan jirgin kasan da ke hanyar zuwa Kaduna daga Abuja dauke da fasinjoji a daren ranar Litinin.

Shehu Sani: Lokaci ya yi da ya kamata a bar 'yan Najeriya su mallaki makami
Shehu Sani: Lokaci ya yi da ya kamata a bar 'yan Najeriya su mallaki makami
Asali: Original

Ana haka, sai hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya a ranar Talata ta sanar da dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna har zuwa wani lokaci sakamakon hare-haren.

Harin jirgin kasan na zuwa ne bayan yan ta’adda kimanin su sama da 200 sun farmaki filin jirgin saman Kaduna da ke yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, inda suka hargitsa harkoki da kuma kashe wani jami’in hukumar NAMA.

Da yake martani kan hare-haren baya-bayan nan a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 31 ga watan Maris, Sani ya bayyana cewa tunda gwamnati ta gaza gurgunta ayyukan yan bindiga, cewa ya kamata a bari mutane su kare kansu da kansu.

Kara karanta wannan

Karin bayani: 'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, sun kashe 9 a jihar Neja

Sani ya rubuta:

“Idan gwamnati da hukumomin tsaro ba za su iya murkushe wadannan yan ta’adda da yan fashi da ke garkuwa da kashe mutanenmu a arewa da kudancin Kaduna ba, ya kamata a baiwa mutane damar daukar makamai a hukumance sannan mu zuba ido mu ga wa ke da kasar.”

Gwamnatin Buhari ga 'yan Najeriya: Ku tarawa 'yan uwanku talakawa da harin jirgi ya shafa kudin magani

A wani labari, ministan sufuri, Mista Rotimi Amaechi, ya bukaci yan Najeriya da su kawo gudunmawar kudi domin kula da wadanda harin jirgin kasa na ranar Litinin ya ritsa da su.

Akalla mutane tara ne suka rasa rayukansu yayin da wasu da dama suka jikkata lokacin da yan bindiga suka far ma jirgin kasan da ke hanyarsa ta zuwa Kaduna daga Abuja.

Amaechi, wanda ya ziyarci wajen harin a ranar Talata, ya ce ba don an toshe sayan manyan kamarori da na’urori na layin dogo da kudinsu ya kai naira biliyan 3 ba, da an dakile harin, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Gwamnati: Har yanzu ba a san adadin mutanen da harin jirgin kasa Abuja-Kaduna ya shafa ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel