Obi na Onitsha: Amsa waya ya hana ni hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa farmaki

Obi na Onitsha: Amsa waya ya hana ni hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa farmaki

  • Mai Martaba Igwe Nnaemeka Alfred Ugochukwu Achebe na Onitsha, ya bayyana yadda ya tsallake rijya da baya bai shiga jirgin Kaduna zuwa Abuja ba
  • Ya sanar da cewa wani kiran waya na minitina kalilan ne ya hana shi bin jirgin saboda an bukaci ya dakata ya halarci wani muhimmin taro
  • A ranar Litinin da ta gataba ne miyagun 'yan ta'adda suka jefa wa jirgin Kaduna zuwa Abuja bam, sannan suka bude masa wuta tare da kisa da sace wasu fasinjoji

Mai martaba Sarkin Onitsha na Jihar Anambra, Mai Martaba Igwe Nnaemeka Alfred Ugochukwu Achebe, ya bayyana yadda ya kubuta daga hawan jirgin Abuja zuwa Kaduna da ‘yan ta’adda suka kai wa farmaki a ranar Litinin, 28 ga watan Maris.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Sarkin zai hau jirgin amma kiran wayar da aka yi masa na wasu mintina yasa ya rasa hawan jirgin.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin Ƙasan Kaduna: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai

Obi na Onitsha: Amsa waya ya hana ni hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa farmaki
Obi na Onitsha: Amsa waya ya hana ni hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa farmaki. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

A wannan rana mai muni ne ‘yan ta’adda suka kai farmaki kan jirgin kasan da ya taho Kaduna. Sun jefa bama-bamai a kan layin dogo, lamarin da ya tilasta wa jirgin tsayawa, Daily Trust ta ruwaito.

Shaidu sun ce daga baya maharan sun kewaye galibin taragwayen jirgin, inda suka bude wuta kafin daga bisani su samu shiga da karfi, sannan suka dinga harbi ba kakkautawa, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wasu daga cikin fasinjojin masu yawa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake magana a lokacin da shugabannin Igbo a karkashin kungiyar Ahamefuna Socio-cultural Organization suka hallara a Enugu, Igwe Achebe ya ce bai hau jirgin ba ne saboda kiran wayar da aka yi masa na gaggawa.

Sarkin ya ce, “Ina cikin fasinjojin da ya dace su shiga jirgin a ranar Litinin da ta gabata, saboda akwai wani taron da ya kamata in halarta. Na riga na kasance a tashar jirgin ƙasa lokacin da aka kira ni don gaggawa kuma dole ne yasa na bar tashar don halartar shi."

Kara karanta wannan

Dalilan Osinbajo na kin yarda Amaechi ya kashe N3.7b wajen tsare hanyar jirgin kasa

Alwan Hassan, Manajan Daraktan BOA, ya yi batan dabo ta harin jirgin kasan Kaduna-Abuja

A wani labari na daban, babu amo ba labarin manajan daraktan bankin manoma (BOA), Alwan Hassan tun lokacin da aka kai wa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna farmaki.

Hassan na ɗaya daga cikin fasinjojin da suka hau jirgin ƙasan Kadunan da aka kaiwa farmaki a ranar Litinin.

The Cable ta ruwaito yadda ƴan bindiga suka yi dirar mikiya ga jirgin ƙasan, inda daga bisani suna kaiwa fasinjoji farmaki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel