Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki

  • Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya bayyana cewa kalubalen tsaro ya mamaye gwamnatin Buhari
  • A cewar Obasanjo, 'yan Najeriya sun rasa tsaro a motoci, jiragen kasa, kai hatta jiragen sama ba su tsira ba yanzu
  • Ya yi kira da a hada kai da masu ruwa da tsaki wurin magance matsalar tunda ta fi karfin mutum daya a halin yanzu

Abeoukuta, Ogun - Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce kalubalen tsaro sun mamaye gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari fiye da zaton mai tunani.

The Punch ta ruwaito cewa, ya bayyana haka ne a lokacin da yake mayar da martani kan harin da aka kai wa jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja da aka tabbatar da mutuwar mutane a kalla mutum 7 tare da batan fasinjoji 21.

Kara karanta wannan

Harin Jirgin Ƙasan Kaduna: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai

Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki
Farmakin jirgin kasa: Obasanjo ya yi martani kan halin da ake ciki. Hoto daga Punchng.com
Asali: UGC

Obasanjo ya ce wannan mummunan al'amari ya nuna cewa ‘yan Najeriya ba su da tsaro a ko’ina – a cikin motoci, a jirgin kasa ko kuma a cikin jirgi. Ya ce kasar na cikin wani mawuyacin hali

Tsohon shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a gidansa da ke dakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, jihar Ogun yayin da ya karbi bakuncin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, Dr Ugochukwu Williams da tawagarsa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Obasanjo ya bayyana damuwarsa kan yadda ‘yan Najeriya ba su da tsaro a kan hanya, a jirgin kasa da kuma a filin jirgin sama, yana mai kira da a hada karfi da karfe da masu ruwa da tsaki don dakile matsalar rashin tsaro a kasar.

Tsohon Shugaban kasar ya bayyana cewa, al’amura sun mamaye gwamnatin da ke yanzu, amma ‘yan Najeriya kada su bari lamarin ya mamaye kasar.

Kara karanta wannan

Ana maganar rufe Majalisa domin tursasa Shugaban kasa ya tashi-tsaye kan lamarin tsaro

Sai dai ya ja kunnen ‘yan Najeriya da kada su bari kalubalen rashin tsaro ya mamaye su, The Punch ta ruwaito.

Ya ce, “Don haka, idan wani ya zo ya ce ina son ganin ku, ina so in yi magana da ku, zan ce ‘barka da zuwa’. Wannan shi ne saboda na yi imani da gaske, kuma na fadi hakan a bainar jama’a, kuma zan sake fadi, halin da muke ciki a kasar nan ba halin da mutum daya zai ce ya magance ba, yana da mafita, sai dai idan muna yaudarar kanmu. Na yi imani ya kamata mu zauna tare mu dubi halin da ake ciki.
"Yanayin da ba ka da tsaro a kan hanya, ba ka da tsaro a cikin jirgin kasa, ba ka da tsaro a filin jirgin sama, yana nuna wani yanayi mai tsanani ne.
"Na yi imanin cewa duk 'yan Najeriya masu tunani dole ne su san cewa akwai mummunan yanayin da ya mamaye gwamnatin yanzu, amma bai kamata mu bar wannan lamarin ya mamaye Najeriya ba."

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Na kaɗu da kashe-kashen dake faruwa a kusa da birnin Abuja, Kwankwaso ya yi magana

Obi na Onitsha: Amsa waya ya hana ni hawa jirgin Abuja zuwa Kaduna da aka kai wa farmaki

A wani labari na daban, Mai martaba Sarkin Onitsha na Jihar Anambra, Mai Martaba Igwe Nnaemeka Alfred Ugochukwu Achebe, ya bayyana yadda ya kubuta daga hawan jirgin Abuja zuwa Kaduna da ‘yan ta’adda suka kai wa farmaki a ranar Litinin, 28 ga watan Maris.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Sarkin zai hau jirgin amma kiran wayar da aka yi masa na wasu mintina yasa ya rasa hawan jirgin.

A wannan rana mai muni ne ‘yan ta’adda suka kai farmaki kan jirgin kasan da ya taho Kaduna. Sun jefa bama-bamai a kan layin dogo, lamarin da ya tilasta wa jirgin tsayawa, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel