Dalilan Osinbajo na kin yarda Amaechi ya kashe N3.7b wajen tsare hanyar jirgin kasa

Dalilan Osinbajo na kin yarda Amaechi ya kashe N3.7b wajen tsare hanyar jirgin kasa

  • Rotimi Amaechi ya nemi a fitar da kudi domin a tsare jirgin kasan Kaduna-Abuja, amma ba ayi ba
  • Ministan sufuri ya zargi gwamnati bayan kai wa jirgin hari, amma an gano asalin gaskiyar lamarin
  • Amaechi ya kawo wani sabon kamfani ne ya bukaci a ba su kwangilar da ake ganin ya fi karfinsu

Abuja - Wata takarda da ta fito ta fallasa abin da ya hana a amince da bukatar Ministan sufuri, na kafa na’urorin tsaro a titin jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja.

Jaridar Punch ta ce Ministan sufurin bai bi ka’ida wajen bada wannan kwangila da za ta ci Naira biliyan 3.7 ba. Hakan ta sa majalisa FEC ta ki karbar rokonsa.

Takardar bayan taron FEC na ranar 24 ga watan Satumban 2021 ya nuna cewa Yemi Osinbajo ya jagorancin zaman FEC a lokacin da aka tattauna a kan batun.

Kara karanta wannan

An sake samun matsala, an rasa rai yayin da wani jirgin kasa ya samu hadari a Kaduna

A daidai wannan lokaci, Mai girma Muhammadu Buhari ya na wajen taron majalisar dinkin Duniya a Amurka, don haka mataimakinsa ya jagoranci FEC.

Mogjan Nigeria Ltd

The Cable ta ce Ministan sufurin ya nemi a bada kwangilar tsare hanyar jirgin ne ga kamfanin Mogjan Nigeria Ltd da a Agustan shekarar 2019 aka kafa shi.

Prince Godwin Momoh, Chioma Momoh da wani George Momoh ne suka bude wannan kamfani. Uwar kudin da kamfanin ke juyawa kuma bai wuce N84.9m.

Osinbajo
Yemi Osinbajo a wajen taro Hoto: @laoluakandeofficial
Asali: Facebook

Hakan ta sa majalisar zartarwar kasar ta ga cewa wannan kamfani da duka bai wuce shekara biyu da fara aiki ba, ba zai iya yin kwangilar biliyoyin kudi ba.

Akwai alamar tambaya

Bugu da kari, ana zargin kamfanin ba su da kwarewar da za su tsare dogon jirgin kasa domin babu abin da ke nuna cewa sun taba yin irin wannan aikin a baya.

Kara karanta wannan

Ya kamata a bar ‘yan Najeriya su rike makamai domin kare kansu, Jigo a majalisar wakilai

Jaridar ta ce an fahimci sai an biya kamfanin wasu kudi na dabam. Ganin haka ta sa majalisar Ministocin tarayya suka ga akwai son kai a harkar kwangilar.

Wata majiya ta ce daga cikin abin da ya sa aka ki amincewa da rokon Ministan sufurin shi ne ya ki bada karin bayani a kan wadannan kayan aikin da za a saya.

Farfesa Yemi Osinbajo da shugaban ma’aikatar fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari sun bukaci cikakken bayani, abin da Ministan sufurin bai iya yi ba.

Amaechi: Mun san za a kawo hari

Kun ji cewa a ranar Talata Ministan sufuri na tarayya ya ziyarci inda ‘yan ta’adda su ka tare jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja, ya ce ai sun yi hasashen za ayi haka.

Rotimi Amaechi ya ce tun farko sai da ya bukaci a kashe N3.7bn wajen sayan wasu kayan tsaro, amma gwamnatin tarayya ta ki amincewa da wannan bukatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel