Alwan Hassan, Manajan Daraktan BOA, ya yi batan dabo ta harin jirgin kasan Kaduna-Abuja

Alwan Hassan, Manajan Daraktan BOA, ya yi batan dabo ta harin jirgin kasan Kaduna-Abuja

  • Ba a sake jin ɗuriyar Manajan daraktan BOA ba, tun lokacin da ƴan ta'adda suka kai wa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna hari a yammacin Litinin
  • Wani jami'in bankin manoma na fannin sadarwa ya bayyana wa manema labarai yadda suka gaza samun wayar Alwan Hassan, wanda shima yana cikin jirgin
  • Duk da babu wanda ya sanar da mutuwarsa, amma an gano yadda mutane da dama suka rasa rayukansu yayin kai harin

Babu amo ba labarin manajan daraktan bankin manoma (BOA), Alwan Hassan tun lokacin da aka kai wa jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna farmaki.

Hassan na ɗaya daga cikin fasinjojin da suka hau jirgin ƙasan Kadunan da aka kaiwa farmaki a ranar Litinin.

Alwan Hassan, Manajan Daraktan BOA, ya yi batan dabo ta harin jirgin kasan Kaduna-Abuja
Alwan Hassan, Manajan Daraktan BOA, ya yi batan dabo ta harin jirgin kasan Kaduna-Abuja. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

The Cable ta ruwaito yadda ƴan bindiga suka yi dirar mikiya ga jirgin ƙasan, inda daga bisani suna kaiwa fasinjoji farmaki.

Kara karanta wannan

Harin jirgin kasan Kaduna-Abuja: Iyalan wasu matafiya na cikin firgici, har yanzu basu ji daga 'yan uwansu ba

An samu labarin yadda mutane da dama, waɗanda suka haɗa da direbobi, masu saida abinci da masu shara suka rasa rayukansu yayin kai harin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Bayan aukuwar lamarin, hoton Hassan ya karaɗe ko ina a kafafan sada zumuntar zamani, musammman WhatsApp.

Tsokacin dake biye da hotun na nuna: "An yi garkuwa da Alwan Hassan a farmakin jirgin ƙasan Kaduna... Muna bukatar addu'oin ku."

Yayin zantawa da The Cable a ranar Talata, wani ma'akacin BOA na sashin sadarwa ya bayyana yadda aka kasa samun Hassan a waya tun bayan aukuwar lamarin.

"Ba mu da tabbacin an yi garkuwa dashi. Eh, a lokacin yana cikin jirgin. Amma har yanzu bamu ji komai daga gare shi ba," a cewar jami'in.

Duk da har yanzu ba'a sanar da mutuwarsa ba, The Cable ta gano yadda fasinjoji da dama suka rasa rayukansu yayin kai harin.

Kara karanta wannan

Abokan Twitter: Likita ta mutu bayan abokai sun karyata hari ya rutsa da ita a Kaduna

Harin jirgin kasan Kaduna-Abuja: Iyalan wasu matafiya na cikin firgici, har yanzu basu ji daga 'yan uwansu ba

A wani labari na daban, wasu daga cikin iyalan fasinjojin dake jirgin ƙasan da ƴan ta'adda suka tare a hanyar Kaduna, ranar Litinin sun ce har yanzu basu san halin da ƴan uwansu ke ciki ba, Daily Nigerian ta ruwaito.

Yayin zantawa da kamfanin dillancin labaran Najeriya a tashar jirgin ƙasan Rigasa cikin Kaduna a ranar Talata, sun bayyana yadda har yanzu basu ji komai game da ƴan uwan nasu ba, bayan awa 14 da aukuwar mummunan lamarin.

Saboda haka, suke roƙon gwamnatin jiha da ta kawo musu ɗauki don su samu sassauci game da fargabar da suke fuskanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel