Harin Jirgin Ƙasa: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai

Harin Jirgin Ƙasa: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai

  • Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya sha alwashin yin hayar sojojin kasar waje don yaki da ‘yan ta’adda
  • Hakan ya biyo bayan farmakin da wasu ‘yan ta’adda suka kai wa jirgin kasa a Kaduna a ranar Litinin da dare
  • Ya kuma ce akwai yiwuwar jihohin arewa maso yamma guda 4, Katsina, Zamfara, Kebbi da Sokoto su bi sahunsa

Abuja - Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya lashi takobin yin hayar sojoji daga kasashen ketare don su taya yaki da ‘yan ta’adda bayan harin da suka kai wa jirgin kasa a Kaduna ranar Litinin.

Ya kuma lissafo jihohi 4 na yankin arewa maso yamma, inda ya ce akwai yuwuwar su bi sahun shi. Jihohin sun hada da Zamfara, Kebbi, Katsina da Sokoto, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ana maganar rufe Majalisa domin tursasa Shugaban kasa ya tashi-tsaye kan lamarin tsaro

Harin Jirgin Ƙasa: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Ɗakko Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai
Harin Jirgin Ƙasa: Idan Sojojin Mu Sun Gaza, Na Rantse, Zan Gayyato Sojojin Haya Daga Kasar Waje – El-Rufai. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce zasu dauki wannan matakin ne matsawar gwamnatin tarayya bata dauki wani matakin a zo a gani ba a yankin.

El-Rufai ya shaida wa manema labaran cikin gidan gwamnati hakan, bayan ya kai wa shugaba Muhammadu Buhari ziyara har fadarsa don sanar da shi batun sabbin hare-heren.

Ya ce in har sojojinmu sun gaza za a gayyato wasu daga kasar waje

Kamar yadda ya shaida:

“Meyasa har yanzu jami’an tsaro basu je sun halakasu ba? Ina sojojinmu? Meyasa suka yi wannan aika-aikar? Shiyasa na kawo wa shugaban kasa wannan ziyarar kuma in har ba a dauki mataki ba, mu za mu dauka.
“A matsayin mu na gwamnoni wajibi ne mu kula da rayukan mutanenmu. Zamu nemi taimakon sojoji daga kasashen waje in har sojojinmu suka gaza, wallahi abinda zamu yi kenan.”

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Na kaɗu da kashe-kashen dake faruwa a kusa da birnin Abuja, Kwankwaso ya yi magana

A cewarsa, bisa ruwayar The Punch, an kai wa jirgin Abuja zuwa Kaduna hari wanda ya ja mutane 8 suka mutu yayin da dayawa suka raunana, kuma ya dace ace gwamnati ta duba alamomi tun kafin ya faru.

Gwamnan wanda aka tattauna da shi da harshen Hausa ya ce ya samu tabbaci daga wurin Buhari cewa za a kawo karshen harin nan cikin ‘yan watanni.

El-Rufai ya ce ‘yan Boko Haram ne suka kai harin

Ya ja kunnen wadanda suka kai harin, inda ya kira su da ‘yan Boko Haram. A cewarsa sai da ya bayar da shawara inda ya ce ya kamata su bar Abuja da misalin karfe 4 na yamma don su isa Kaduna da wuri.

Tsohon ministan Abujan ya kula da yadda harin ya bambanta da sauran hare-haren da aka saba kaiwa.

Ya ce ya kamata a dinga bin ‘yan bindiga ana harbinsu ba tare da an jira sun shigo cikin mutane har sun kai hari ba.

Ta bayar da tabbaci akan yadda shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai kawo karshen hare-hare nan da ‘yan watanni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel