Masu Garkuwa Da Ake Nema Ruwa a Jallo Saboda Fitinar Mazauna Kano Da Jigawa Sun Miƙa Kansu Ga Ƴan Sanda

Masu Garkuwa Da Ake Nema Ruwa a Jallo Saboda Fitinar Mazauna Kano Da Jigawa Sun Miƙa Kansu Ga Ƴan Sanda

  • Wasu shu'uman masu garkuwa da aka dade ana nema ruwa a jallo saboda adabar mutanen Kano da Jigawa sun mika wuya
  • Yusuf Wakili, shugaban masu garkuwar tare da wasu yan tawagarsa hudu sun mika kansu da makamansu ne ga Kwamandan Yan sandan Ringim, MK Abdullahi
  • Hakan ya faru ne sakamakon bin sahunsu da yan sandan suka yi har ta kai sun ritsa su ba su da mafita dole suka mika wuya tare da bindigunsu

Jigawa - Wasu masu garkuwa da mutane su hudu da ke adabar mazauna jihohin Jigawa da Kano sun mika kansu ga 'yan sanda, a cewar yan sandan Jihar Jigawa, rahoton Premium Times.

Kakakin yan sandan jihar, Lawan Adam, ya ce kwamandan yan sandan karamar hukumar Ringim, MK Abdullahi ne ya bi sahun sun yan ta'addan, kafin suka mika wuya tare da makamansu.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya ya fadawa ‘Yan Najeriya su kauracewa zaben Atiku, Tambuwal, Saraki da Obi

Masu Garkuwa Da Ake Nema Ruwa a Jallo Saboda Fitinar Mazauna Kano Da Jigawa Sun Miƙa Kansu Ga Ƴan Sanda
Masu Garkuwa Da Mutane Sun Miƙa Kansu Ga Ƴan Sanda a Jigawa. Hoto: Vanguard.
Asali: UGC

Mr Adam ya ce masu garkuwar, karkashin jagorancin Yusuf Wakili, mai shekaru 30, mazaunin Ajingi a Kano, ya mika AK-47 guda daya da harba ka gudu guda biyu.

"A ranar 26/03/2022 bayan samun bayanan sirri, kwamandan yan sandan Ringim, ACP MK Abdullahi da tawagarsa sun bi tare da kama wani hatsabiban mai garkuwa, Yusuf Wakili aka Rago, mai shekaru 30 mazaunin karamar hukumar Ajingi a Kano.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya mika wuya tare da yan tawagarsa hudu masu suna; Inusa Jibrin, 30, Tahir Zango, 27, yan karamar hukumar Ajingi. Sabo Abdullahi Alias Sabo Gara, 35, mazaunin Gerawa, karamar hukumar Ringim na Jigawa da Suleiman Garba, Alias Manu Dogo, mazaunin Wangara, a karamar hukumar Dutse, Jihar Jigawa,” in ji kakakin yan sandan.

Wadanda ake zargin sun yi garkuwa da mutane da dama tare da fashi da makami a jihohin Jigawa da Kano, ya kara da cewa kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Sace Jami'in Kwastam, Ɗansa Da Wasu Mutum 8 a Sabuwar Harin Da Suka Kai a Kaduna

Mr Adam ya ce an mika wadanda ake zargin ga sashin binciken manyan laifuka inda ake musu tambayoyi.

Ya ce suna bada hadin kai kuma suna bada bayanai masu amfani da zai taimaka a kama abokan harkallarsu.

'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci

A bangare guda, Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.

A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel