'Yan Bindiga Sun Sace Jami'in Kwastam, Ɗansa Da Wasu Mutum 8 a Sabuwar Harin Da Suka Kai a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Sace Jami'in Kwastam, Ɗansa Da Wasu Mutum 8 a Sabuwar Harin Da Suka Kai a Kaduna

  • Miyagun yan fashin daji sun kai hari a unguwar Kofan Gayan Low Cost da ke Zaria a Jihar Kaduna
  • Maharan sun sace wani jami'in hukumar yaki da fasakwabri, Gambo Turaki, dansa Khalifa da wasu mutane takwas
  • Daga bisani hudu daga mutanen da yan bindigan suka yi garkuwa da su sun tsere sun dawo gida, sun ce sha tafiya a daji

Zaria, Kaduna - An sace wani jami'in kwastam mai suna Gambo Turaki da wasu mutane tara a Kofar Gayan Low-Cost Zaria a Jihar Kaduna.

Daily Trust ta rahoto cewa yan bindigan sun afka wurin ne misalin karfe 9 na daren ranar Laraba.

Wannan shine karo na biyu da yan bindiga ke kai hari Kofan Gayan Low Cost suna sace mutane.

Kara karanta wannan

Wasu masu laifi sun tsere daga Ofishin yan sanda a Gombe

'Yan Bindiga Sun Sace Jami'in Kwastam, Ɗansa Da Wasu Mutum 8 a Sabuwar Harin Da Suka Kai a Kaduna
'Yan Fashin Daji Sun Sace Jami'in Kwastam, Ɗansa Da Wasu Mutum 8 a Sabuwar Harin Da Suka Kai a Zaria. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

A bara, yan bindiga sun kutsa unguwar sun sace matar wani jami'in kwastam da wata mata, sun sako su bayan an biya fansar N15m.

Dagacin unguwar Kofan Gayan, Muhammadu Nazifi ya magantu game da harin

Da ya ke tabbatarwa Daily Trust afkuwar lamarin, dagacin unguwar, Muhammadu Nazifi ya ce wadanda aka sace sun hada da dansa Jamalu, jami'in kwastam, Mu'awiyya Gambo Turaki wanda ya dawo daga aiki a jiya da dansa Khalifa.

Ya kara da cewa, "Sun kuma sace wata mata Jamila Usman da wani yaro mai suna Khalifa.
"Amma, hudu daga cikinsu sun tsere sun dawo gida."

A bangarensa, daya cikin wanda suka tsere daga hannun yan bindgan, Yushau Isah ya ce sun yi nasarar tserewa ne bayan sunyi tafiyar kimanin kilomita 5 a cikin daji da yan bindigan.

Kara karanta wannan

Jerin sunaye da bayanan mutanen da suka mutu a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Ya ce:

"Maharan sun kai su takwas kuma da kafa suka taho da muggan makamai. Sun yi kokarin magana da mu da Hausa amma Fulatanci suke yi."

Isah ya ce da duhun dare suka tsere

"Muna zargin wasu ne suka kai musu bayanai na sirri domin bisa ga alamu jami'in kwastam din da ya dawo daga aiki a jiya suke so kama wa," in ji shi.

Daily Trust ta rahoto cewa jami'an tsaro sun amsa kirar da aka musu amma sun yi lati kadan domin ko da suka iso yan bindigan sun tafi da wadanda suka sace.

'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci

A wani labarin, Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Yanzu Nan: IGP da Shugaban Sojoji zasu je wurin da yan bindiga suka ɗana wa Jirgi Bam a Kaduna

A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel