An san su, an gaza kama su: Shehu Sani ya bayyana sunayen shugabannin 'yan bindigan da suka addabi Arewa

An san su, an gaza kama su: Shehu Sani ya bayyana sunayen shugabannin 'yan bindigan da suka addabi Arewa

  • Tsohon dan majalisar dokoki daga Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana sunayen wasu jagororin ta’addanci da aikata barna a yankin Arewa
  • Sani ya yi zargin cewa sunayen ‘yan ta’addan sun kusa cike gidajen 'yan Arewa, inda ya ce suna yawo cikin walwala ba tare da tsangwama ba
  • Fitaccen dan siyasar ya kuma lura da cewa, 'yan ta'addan na hira da gidajen rediyo da jaridu cikin harshen Hausa

Shehu Sani ya bayyana sunayen manyan ‘yan ta’adda a yankin Arewa da ake zargin su ne ke yawo cikin walwala da aiwatar da hare-haren ta’addanci a yankin.

Legit.ng ta tattaro cewa tsohon sanatan daga Kaduna ta tsakiya ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Alhamis, 31 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Jirgin yaƙin Sojojin Najeriya ya halaka dandazon yan bindiga a bodar Kaduna da Neja

Shehu Sani ya ambaci sunayen 'yan ta'adda
Shehu Sani ya tona asirin wasu da ake zargin shugabannin ta'addanci ne da ke aiki a arewa | Hoto: Olubiyo Samuel
Asali: UGC

Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ta 8 ya bayyana sunayen manyan shugabannin ta'addancin Arewa kamar su Bello Turji, Dogo Gide, Manjagara, da Baleri.

Ya kuma yi mamakin yadda wasu jagororin ta’addanci a Arewa, wadanda suka kusan sunayensu suka zama sanannu gidaje ke ci gaba da yawo kana hukumomi suka gagara kama su.

A cewarsa, wadanda ake zargin shugabannin ‘yan ta’adda ne, amma kuma suke samun damar hira da gidajen rediyo da jaridu cikin harshen Hausa.

Ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa:

“Bello Turji, Dogo Gide, Manjagara da Balleri sune gawurtattun jagororin ‘yan ta’adda na Arewa wadanda suka yi hira da gidajen rediyo da jaridu a cikin harshenmu na Hausa, amma har yanzu ba su san yadda hukumomi za su kama su ba. Ni dai ban gane ba."

Kara karanta wannan

Karar kwana: 'Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye

Yan bindigan sun kai hari gidan Kwamishinan jiha, sun tada bama-bamai

A wani labarin, wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun kai hari tare da abubuwan fashewa gidan kwamishinan kwadugo na jihar Imo, Ford Ozumba, da safiyar Jumu'an nan.

Yan bindigan sun kai wannan harin ta'addancin ne a gidansa dake mahaifarsa Umuhu, yankin Okabia, ƙaramar hukumar Orsu a jihar ta Imo.

Kwamishinan ne ya tabbatar da haka ga jaridar Vanguard a Owerri, inda ya ƙara da cewa yan uwansa dake zaune a can ne suka sanar da shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel