Da Dumi-Dumi: Yan bindigan sun kai hari gidan Kwamishinan jiha, sun tada bama-bamai

Da Dumi-Dumi: Yan bindigan sun kai hari gidan Kwamishinan jiha, sun tada bama-bamai

  • Yan bindiga da ba'a gane su waye ba sun kai hari da abubuwan fashewa a gidan Kwamishinan Kwadugo na jihar Imo
  • Kwamishinan ne ya tabbatar da haka da safiyar Jumu'a, ya ce babu wanda ya rasa ransa amma sun lalata gidan da Bam
  • Kakakin hukumar yan sanda ta jihar Imo, Micheal Abattam, ya ce ba su da masaniyar abin da ya faru a hukumance

Imo - Wasu yan bindiga da ba'a san ko suwaye ba sun kai hari tare da abubuwan fashewa gidan kwamishinan kwadugo na jihar Imo, Ford Ozumba, da safiyar Jumu'an nan.

Yan bindigan sun kai wannan harin ta'addancin ne a gidansa dake mahaifarsa Umuhu, yankin Okabia, ƙaramar hukumar Orsu a jihar ta Imo.

Kwamishinan ne ya tabbatar da haka ga jaridar Vanguard a Owerri, inda ya ƙara da cewa yan uwansa dake zaune a can ne suka sanar da shi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: IBB ya gana da 'yan takarar shugaban kasa 4 daga yankin Arewa

Taswirar jigar Imo.
Da Dumi-Dumi: Yan bindigan sun kai hari gidan Kwamishinan jiha, sun tada bama-bamai Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ya bayyana cewa babu wanda ya rasa rayuwarsa amma Bama-Baman da maharan suka jefa ya ragargaza gidan baki ɗaya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A kalamansa kwamishinan ya ce:

"Ina Owerri, suka kira ni da Safe kuma suka shaida mun an kai wa gidana hari da Safiyar nan. Sun jefa abubuwan fashewa a ciki, gidan ya ƙone. Babu wanda ya mutu amma gidan ya ƙone."

Shin hukumomi sun san abin da ya faru?

Da aka tuntube shi, kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Imo, Micheal Abattam, ya ce rundunar yan sanda ba ta da masaniyar abin da ya auku a hukumance.

Idan baku mance ba, a shekarar da ta gabata, yan bindigan sun farmaki gidan kwamishinoni a jihar Imo.

Daga cikin waɗan da aka kai wa gidajen su hari, akwai Kwamishinan yaɗa labarai da dabaru, Declan Emelumba, da kwamishinan Shari'a kuma Antoni Janar na jihar, Cyprian Akaolisa.

Kara karanta wannan

Karar kwana: 'Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye

A wani labarin na daban kuma An sake gano wani Bam da aka ɗana a Kaduna, awanni bayan warware wani

Mutane sun sake gano wani abun fashewa a yankin Shanono dake Anguwar Rigasa karamar hukumar Igabi ta Kaduna.

Wani mazaunin yankin ya ce kananan yara ne suka fara gano Bam ɗin a cikin Jarka a wurin da aka ga na jiya Alhamis.

Asali: Legit.ng

Online view pixel