Yanzun Nan: Jirgin yakin sojojin Najeriya ya halaka yan ta'adda 34 a bodar Kaduna da Neja

Yanzun Nan: Jirgin yakin sojojin Najeriya ya halaka yan ta'adda 34 a bodar Kaduna da Neja

  • Sojojin Najeriya sun sheƙe yan ta'adda aƙalla 34 a wani ƙauye dake iyaka tsakanin jihar Kaduna da Neja
  • Majiyar Sojoji ta bayyana cewa sun samu bayanan sirri na ganin yan ta'adda 70 a kan babura 40 wasu kuma aƙasa sun nufi hanyar Akilibu – Sarkin Pawa
  • Daraktan watsa labarai na rundunar NAF ya tabbatar da cewa Jiragen su na aikin kai hari yankin kuma suna yin nasara

Niger - Jirgin yaƙin rundunar sojin Najeriya ya gano tare da aika yan ta'adda 34 lahira a ƙauyen Mangoro, yankin da ya yi iyaka tsakanin jihar Kaduna da Neja.

Leadership ta rahoto cewa Sojin sun samu bayanin cewa an ga yan ta'adda kusan 70 a kan Babura 40 da wasu a ƙafa sun nufi hanyar Akilibu – Sarkin Pawa, a ranar 30 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

Nasara Daga Allah: Sojoji sun samu gagarumar nasara kan Boko Haram/ISWAP a wani gumurzu

Dakarun rundunar sojin Najeriya.
Yanzun Nan: Jirkin yakin sojojin Najeriya ya halaka yan ta'adda 34 a bodar Kaduna da Neja Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Majiya daga cikin dakarun sojin ya bayyana cewa bayan samun bayanan sirri na yan ta'adda, Dakarun sojin sama na Operation Thunder Strike, suka tashi jirgi ya bibiyi lamarin kuma ya musu luguden wuta.

Ya ce:

"Jirgin yaƙin ya nufi wurin kai tsaye, nan take yaga yan ta'adda da yawa suna kokarin guduwa biyo bayan ganin zuwan Jirgin da nufin ɓuya a dazukan dake kusa."
"Ba ɓata lokaci ya fara musu ruwan wuta ta kowane ɓangare da makamin Roka yayin da waɗan da ke kokarin tserewa aka tarbo su ba ƙaƙƙauta wa."
"Bayanan da muka samu daga kauyen Mangoro ya bayyana cewa an gano Babura 17, gawarwaki 34 da kuma bindigu 14 mallakin yan ta'addan."

Shin yan ta'addan na da alaƙa da harin jirgin ƙasa a Kaduna?

Kara karanta wannan

Neja: Yadda Kwale-Kwale ya nutse da mata da kananan yara yayin guduwa daga harin yan bindiga

Sai dai majiyar ba ta tabbatar da cewa ko yan ta'addan ne suka kai hari kan jirgin ƙasa a hanyar Abuja-Kaduna ranar Litinin da daddare.

"Babu tabbacin ko yan ta'addan ne suka kai wa jirgin ƙasa kuma suka kashe Fasinjoji 8 a hanyar Kaduna kwanakin nan da suka wuce."

Mutanen yankin sun yaba wa sojojin bisa ƙara kaimi wajen ɗaukar matakin gaggawa da zaran an basu bayanai.

Kazalika sun roki dakarun sojin sun ƙara matsa kaimi wajen kamo waɗan da ke da hannun a kisan Fasinjojin jirgin ƙasa.

Da aka tuntuɓi daraktan hulɗa da jama'an da rundunar sojin sama, Air Cdre Edward Gabkwet, ya tabbatar da cewa Jiragen NAF na kai hare-hare yankin kuma suna samun nasara.

A wani labarin kuma Yan bindiga sun ƙone Sakatariyar karamar hukuma a jihar Anambra

Wasu yan bindiga sun kona Sakatariyar karamar hukumar Nnewi South a jihar Anambra, mutum ɗaya ya rasa rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Alwan Hassan, Manajan Daraktan BOA, ya yi batan dabo ta harin jirgin kasan Kaduna-Abuja

Wani shaida ya tabbatar da cewa Mai gadin wurin ne ya mutu, mutane sun shiga yanayin tashin hankali a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel