Kano: Matasa Da Mata Sun Yi Karo-Karo Sun Siya Wa Rimingado Fom Din Takara Don Ya Gaji Kujerar Ganduje a 2023

Kano: Matasa Da Mata Sun Yi Karo-Karo Sun Siya Wa Rimingado Fom Din Takara Don Ya Gaji Kujerar Ganduje a 2023

  • Wata kungiya da ke kiran kanta 'Concerned Citizens of Kano', ta siya wa dakataccen Shugaban hukumar yaki da rashawa na Jihar Kano, Muhyi Rimingado fom din takarar gwamna a Kano
  • Kungiyar ta ce matasa ne daga kananan hukumomi daban-daban suka hada kudi suka siya wa tsohon shugaban hukumar yaki da rashawar ta Kano fom din
  • Yayin gabatar masa fom din a Abuja, shugaban kungiyar, , Malam Nafiu Danlami ya ce sunyi imanin Rimingado ne ya cancanci zama gwamna suna kuma kira gare shi ya amsa kiransu

FCT, Abuja - Wata kungiya, 'Concerned Citizens of Kano', a ranar Alhamis, ta siya wa tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa na Kano, Muhyi Rimingado, fom din takarar gwamna a PDP.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya ya fadawa ‘Yan Najeriya su kauracewa zaben Atiku, Tambuwal, Saraki da Obi

Shugaban Kungiyar, Malam Nafiu Danlami, ya gabatar da fim din ga Rimingado a Abuja a ranar Alhamis, yana bukatar shi (Rimingado) ya ayyana niyarsa na yin takarar, rahoton The Punch.

Kano: Matasa Da Mata Sun Yi Karo-Karo Sun Siya Wa Rimingado Fom Din Takara Don Ya Gaji Kujerar Ganduje a 2023
Kano: Matasa Sun Siya Wa Rimingado Fom Din Takara Don Ya Gaji Kujerar Ganduje a 2023. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Danlami ya ce matasa daga kananan hukumomin Kano ne suka bada tallafin dubu dai-dai don ra'ayin kansu don siyan fom din domin sun yi imani da adalci da cancanta na Rimingado ya jagoranci Kano.

"Daruruwan matasan Kano da mata sun hada kansu sun siya fom din nuna sha'awa da ne neman takarar gwamna ga tauraronmu saboda sun yarda da gaskiyarsa da rikon amana.
"Mun yi imanin cewa shine irin dan takarar da Jihar Kano ke bukata domin tafiyar da harkokinta. Mun san dukkan matsalolin da ke adabar Najeriya, musamman yankinmu, wato Jihar Kano.

Kara karanta wannan

N30,000: Sanatan APC Goje ya baiwa matasa da mata sama da 2,000 tallafin dogaro da kai

"Matasan da mata sun hada kansu kuma muna cikin shiri domin zaben Rimingado," in ji shi.

Tsohon shugaban hukumar yaki da rashawar ta Jihar Kano ya ce tun bayan da aka dakatar da shi a Yulin 2021, ya rika fuskantar barazana, cin fuska da bita da kuli da barazana ga rayuwarsa a Kano.

2023: Zan iya shugabancin Najeriya amma dai ban matsu ba, Orji Kalu

A wani labarin, bulaliyar Majalisar Dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce duk da a shirye ya ke da ya yi kamfen kuma zai iya shugabantar kasar nan, amma bai matse ya ce ai zama shugaban Najeriya ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kalu, tsohon gwamnan Jihar Abia, ya yi wannan bayanin ne a ranar Laraba yayin amsa tambayoyi daga manema labarai a Majalisar Tarayya, washegarin da ya kai wa Buhari ziyara a fadarsa da ke Abuja.

A cewarsa kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, takarar shugaban kasa hukunci ne ‘yan Najeriya zasu yanke sannan ko wacce jam’iyya zata zabi bangaren da za ta bai wa damar tsayawa takara, musamman jam’iyyar APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel