Asusun banki a Najeriya yanzu ya zarce yawan jama'ar Ghana da kasashe 11 na Afirka

Asusun banki a Najeriya yanzu ya zarce yawan jama'ar Ghana da kasashe 11 na Afirka

  • NIBSS ta bayyana cewa an bude sabbin asusu na banki miliyan 66.6 a Najeriya cikin shekaru biyu
  • An bude sabbin asusun ne tsakanin Disamba 2019 zuwa Disamba 2021 yayin da bankuna ke yin amfani da sabbin fasaha sosai
  • A cewar babban bankin Najeriya (CBN), akwai bankunan kasuwanci guda 23 da aka basu izinin gudanar da aiki a kasar

Alkalumman baya-bayan nan da hukumar kula da harkokin bankunan Najeriya (NIBSS) ta fitar ya nuna cewa adadin asusun ajiyar a Najeriya ya kai miliyan 191.4 a karshen watan Disambar 2021.

Wannan karin miliyan 66.6 kenan daga jimillar asusun ajiyar banki da ya kai miliyan 118.1 a karshen watan Disambar 2019.

Adadin asusun banki a Najeriya
Asusun banki a Najeriya yanzu ya zarce yawan jama'ar Ghana da kasashe 11 na Afirka | Hoto: businessday.ng
Asali: Getty Images

Duk da haka, akwai bambanci mai tarin yawa tsakanin adadin masu asusun da kuma asusu masu aiki dasu a Najeriya.

Kara karanta wannan

EFCC ta damke wasu matasa shida kan zargin sace wa Kakarsu kudi a jihar Kano

A bisa bayanan NIBSS, daga cikin asusun ajiyar banki miliyan 191.4 a kasar nan, asusu miliyan 133.5 ne kacal, wato kashi 69.74% ke aiki ya zuwa karshen 2021.

Jumillar yawan asusun na banki ya nuna akwai asusu miliyan 49.8 na 'Current', asusun ajiyar kudi na 'savings' miliyan 120.4, asusun kamfanoni na 'corporate' miliyan 8.9 da kuma asusun mutane daidaiku miliyan 179.2.

Asusun banki a Najeriya/Yawan jama'a a kasashen Yammacin Afirka

Sabbin bayanan NIBSS na adadin asusun ajiyar banki a Najeriya, abin sha'awa, ya nuna cewa idan da za a kwatanta adadin asusun banki a Najeriya da al'ummar wata kasa, zai zarce yawan al'ummar kasashen Yammacin Afirka 11.

Kasashen sun hada da Ghana, Ivory Coast, Senegal, Togo, Mali, Benin, Liberia, Nijar, Guinea da Saliyo.

Kara karanta wannan

Adadin talakawan da ke rayuwa Najeriya ya na tashi, zai kai miliyan 95 a shekarar nan

A dunkule yawan al'ummar kasashen da aka ambata a sama a cewar bayanan Worldmeter, an kiyasta adadinsu ya kai miliyan 172.83 wanda ya yi kasa da adadin asusun banki miliyan 191.4 da 'yan Najeriya ke dashi.

Yawan al'ummar kasashen yammacin Afirka

  1. Ghana 32,253,975
  2. Ivory Coast 27,513,793
  3. Senegal 17,510,912
  4. Togo 8,616,046
  5. Mali 21,264,605
  6. Benin 12,675,167
  7. Laberiya 5,264,344
  8. Nijar 25,729,079
  9. Guinea 13,751,974
  10. Saliyo 8,259,046

Bankuna a Najeriya sun fara jan cajin USSD N6.98, masana sun bayyana illar haka

A wani labarin, wasu bankuna sun sanar da kwastomominsu cewa za su fara cajin su N6.98 a kowane mu’amala ta USSD da suka yi, Punch ta ruwaito.

Sai dai, masana sun ce yawan cajin da bankuna ke yi na iya zama barazana ga shigar da kudi.

A cewarsu, zai kara hada-hadar kudi a hannu saboda yawancin kwastomomin banki za su guji amfani da USSD a ma'amalolin yau da kullum.

Kara karanta wannan

Sojoji sun yi kaca-kaca da maboyar 'yan ta'addan IPOB, sun kwato muggan makamai

Asali: Legit.ng

Online view pixel