Adadin talakawan da ke rayuwa a Najeriya ya na tashi, zai kai miliyan 95 a shekarar nan

Adadin talakawan da ke rayuwa a Najeriya ya na tashi, zai kai miliyan 95 a shekarar nan

  • Babban bankin Duniya ya ce an dauki lokaci ba a iya tsamar da al'umma daga kangin talauci ba
  • Hasashe ya nuna talakawan da su ke zaune a kasar Najeriya sun kara yawa, sun doshi miliyan 95.1
  • Daga 2015 abubuwa su ka kara yin muni, sannan annobar cutar COVID-19 ta kara talauta Bayin Allah

Nigeria - Babban bankin Duniya ya ce ana cigaba da fama da matsalar talauci a Najeriya, tun 2015 kuma ba a iya rage yawan masu fadawa cikin talauci ba.

Bankin Duniyan ya bayyana cewa wadanda suke burmawa cikin kullin talauci su na kara yawa. Wannan rahoto ya zo a jaridar Punch a ranar Larabar nan.

Babban bankin da ke birnin Washington a kasar Amurka ya yi hasashen yawan talakawan Najeriya zai karu zuwa mutum miliyan 95.1 a shekarar nan.

Kara karanta wannan

Amaechi: Dama na yi hasashen za a kawo hari a jirgi, na nemi kayan tsaro amma aka hana

Wannan bayani ya na cikin rahoton da masanan bankin Duniyan su ka yi wa take da ‘A Better Future for All Nigerians: 2022 Nigeria Poverty Assessment’.

Yunkurin ceto talakawa ya ci tura

“Kubutar da mutane daga cikin talauci a Najeriya a shekaru goman da suka wuce ya tsaya cak kamar yadda duk wasu bincike da safiyonmu suka nuna.”
“Hasashen da muka gudanar ya nuna mutanen da ke cikin kangin talauci a 2010 ya kai 42.8%. Wannan ya yi kasa da binciken GHS da aka yi a 2010/11.”
Talakawan da ke rayuwa Najeriya
'Ya 'yan talakawa a Najeriya Hoto: www.mediaissuesng.com
Asali: UGC

“Talauci ya ragu kadan ne a shekaru goma da suka wuce, adadin talakawa sun kara yawa, idan aka yi la’akari da yadda mutanen Najeriya ke kara yawa.”

- Rahoton bankin Duniya

Matsin lambar Najeriya a 2016

Kara karanta wannan

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

A cewar bankin, talauci ya soma raguwa bayan 2010, amma daga nan sai lamarin ya jagwalgwale a 2015. daga nan tattalin arzikin Najeriya ya tabarbare sosai.

Rahoton ya ce hakan bai zo da mamaki ba domin karfin tattalin arzikin kasar nan ya tsuke a 2016, inda aka shiga cikin matsin lamba a dalilin karyewar mai.

Annobar COVID-19 ta kara yawan talakawan Najeriya da mutum miliyan biyar a 2022. Da farko mutum miliyan 90 aka yi tunanin za su tsiyace a cikin bana.

Yanzu ana tunanin adadin marasa karfi zai kai miliyan 95.1. A 2018/19, yawan talakawan ba su wuce miliyan 82.9 ba, a 2020 ne su ka karu zuwa miliyan 85.2

'Yan siyasa su na cabawa a Najeriya

Duk da kukan rashin kudi, a makon nan aka ji cewa kudin da jam’iyyar PDP ta ke samu daga saida fam din shiga takarar shugaban kasa ya kai N285m.

Kara karanta wannan

Da dumi: Jihar Kaduna ta sake daukar dumi yayin da yan bindiga suka kashe mutum 50, sun yi awon gaba da wasu

A zaben 2023, jam’iyyar hamayyar ta yi wa takardar neman tikitin shugaban kasa kudi a kan N40m. Mutane akalla takawas kuma sun saye wannan fam.

Asali: Legit.ng

Online view pixel