Bankuna a Najeriya sun fara jan cajin USSD N6.98, masana sun bayyana illar haka

Bankuna a Najeriya sun fara jan cajin USSD N6.98, masana sun bayyana illar haka

- Bankuna a Najeriya sun bayyana cewa, tuni sun fara janye N6.98 ga duk wanda ya yi hulda da USSD

- USSD dai shine tsarin amfani da lambobi a wayar salula don aika kudi da sauran mu'amalar banki

- Wasu 'yan Najeriya sun koka game wannan sabon tsari, tare da yin ishara ga illar irin wannan tsarin

Wasu bankuna sun sanar da kwastomominsu cewa za su fara cajin su N6.98 a kowane mu’amala ta USSD da suka yi, Punch ta ruwaito.

Sai dai, masana sun ce yawan cajin da bankuna ke yi na iya zama barazana ga shigar da kudi.

A cewarsu, zai kara hada-hadar kudi a hannu saboda yawancin kwastomomin banki za su guji amfani da USSD a ma'amalolin yau da kullum.

Hakazalika, akwai yiyuwar hakan ya sanyaya gwiwar bangaren mutanen da ba su da asusun banki saboda ba za su so biyan irin wadannan kudade a kan 'yan kudaden da za su ajiye ba.

KU KARANTA: Jinkirta Sallar Asuba ya sa Sheikh Sudais ya tube shugaban limamai a Saudiyya

'Yan Najeriya sun fara kokawa kan cire musu N6.98 na USSD a banki
'Yan Najeriya sun fara kokawa kan cire musu N6.98 na USSD a banki Hoto: techzim.co.zw
Asali: UGC

Bankunan sun bukaci kwastomomin da su yi amfani da wasu hanyoyin ma'amaloli na yanar gizio ko na'ura don kaucewa biyan kudaden.

Wani tsohon Shugaban Kungiyar Akantocin Najeriya, Dokta Sam Nzekwe, ya ce sauye-sauye da yawa da bankuna suka yi ba sa maraba da harkar hada-hadar kudi, musamman ga ’yan Najeriya da ba sa hulda da banki.

Ya ce mutane za su gwammace su shigo har harabar banki don biyan kudi da ajiya fiye da su bari a janye musu dan kudaden da suke dashi.

“Akwai caji da yawa da bankunan ke cajin kwastomomi, ko da kuwa ba ka yi wata mu’amala dasu ba.

"Wasu daga cikin gama garin mutane za su fara gujewa banki saboda ba za su iya fahimtar yawancin irin wannan cajin ba. Wannan shine dalilin da ya sa yawancin mutane suke yin harkarsu da tsabar kudi.

Ya ce ya kamata bankuna su kasance masu budewa tare da bayyanawa kwastomominsu gaba daya halin da suke ciki wajen hulda dasu, Economic Confidential ta ruwaito.

Wani mai sana’ar dinka kayayyaki, Balogun, ya ce, “Ina da asusun banki amma na fi son in je banki in yi abubuwa na. Nawa ne a cikin asusu na da suke son suke cire kudi ba gaira ba dalili? ”

KU KARANTA: Wata sabuwa: Kasar Morocco ta halasta noman tabar wiwi a fadin kasar

A wani labarin, Babban Bankin Duniya ya sake nazarin bunkasar tattalin arzikin da Najeriya ta yi hasashe, wanda ya kara kimanta yawan kayan cikin gida na 2021 zuwa 1.8%.

Cibiyar Bretton Wood ta daga ci gaban tattalin arzikin Najeriya daga 1.1% zuwa 1.8% na wannan shekarar, yayin da ta bayyana cewa GDP zai kara karuwa zuwa 2.1% a shekara mai zuwa, da kuma 2.4% a shekarar 2023 ta badi.

Tattalin arzikin Afirka kuwa an sake daga shi zuwa sama har 2.8% a shekarar 2021, kuma a shekara mai zuwa, tattalin arzikin yankin ana hasashen zai kai 3.3%. An kiyasta tattalin arzikin duniya cewa zai tashi da kashi 5.6%.

Asali: Legit.ng

Online view pixel