EFCC ta damke wasu matasa shida kan zargin sace wa Kakarsu kudi a jihar Kano

EFCC ta damke wasu matasa shida kan zargin sace wa Kakarsu kudi a jihar Kano

  • EFCC ta samu nasarar chafke wasu matasa bisa zargin sace wa kakarsu kudi
  • An damke sune a wurare daban daban tsakanin 6 da 7 ga watan Maris 2022
  • Daya daga cikinsu ne ya samu masarar kutse cikin asusun bankin kakar

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin azikin kasa zagon kasa, EFCC ta damke wasu matasa shida da ake zargi da sace wa kakarsu miliyan N15.7 a jihar Kano.

Wadanda ake zargin Badaru Munir (23); Aliyu Falalu ( 23); AlMustapha Nasir( 22); Haruna Salisu Abatua( 23); Ismail Salisu Jibia (22), Ishaq Aminu (19), an damke su ne a wurare daban daban tsakanin 6 da 7 ga watan Maris, 2022.

Kara karanta wannan

An Gurfanar Da Wani Mutum a Kotu Kan Satar Biskit Na N1,250 Daga Kanti

An samu nasarar kama sune bayan wani Abdullahi Umar ya kai korafi cewa, wani lokaci a Satumba 2021, an cire kimanin N15, 708, 940 daga asusun bankin Union bank sannan aka tura shi izuwa wasu asusun banki daban daban.

EFCC ta damke wasu matasa shida kan zargin sace wa Kakarsu kudi a jihar Kano
EFCC ta damke wasu matasa shida kan zargin sace wa Kakarsu kudi a jihar Kano Source: Facebook
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

EFCC ta damke wasu matasa shida kan zargin sace wa Kakarsu kudi a jihar Kano
EFCC ta damke wasu matasa shida kan zargin sace wa Kakarsu kudi a jihar Kano Source: Facebook
Asali: Facebook

EFCC ta damke wasu matasa shida kan zargin sace wa Kakarsu kudi a jihar Kano
EFCC ta damke wasu matasa shida kan zargin sace wa Kakarsu kudi a jihar Kano Source: Facebook
Asali: Facebook

Daya daga cikinsu ne ya sace layin wayar Kakar

Binciken EFCC ya nuna cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin, Almustapha Nasir, ya sace layin wayar kakar tashi ne da kuma lambar wayar da take amfani dashi na asusun bankin ta, sannan ya bawa daya daga cikinsu, Hamza wanda ya kware a kutse cikin asusun bankin mutane.

Bayan kutsen da Hamza yayi ne sai aka cire duka kudin asusun bankin kakar.

Wasu masu laifi sun tsere daga Ofishin yan sanda a Gombe

Kara karanta wannan

Karar kwana: 'Yan bindiga sun kai hari Zamfara, sun kashe mutane da dama ciki har da hakimin kauye

A wani labarin kuma, Akalla masu laifi biyar ne suka tsere daga ofishin yan sanda dake yankin Awak dake karamar hukumar Kaltango a jihar Gombe.

Uku daga cikin wanda ake zargin an kama su, amma sauran biyu ana neman su har yanzu a lokacin hada wannan rahoton, kamar yadda The punch ta ruwaito.

Wannan na kunshe cikin wani jawabin manema labarai wanda mai magana da yawun hukumar yan sanda, Mahdi Abubakar ya sanyawa hannu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel