2023: Lokaci yayi da Kudu zata fito da dan takarar Shugaban Kasa, CAN

2023: Lokaci yayi da Kudu zata fito da dan takarar Shugaban Kasa, CAN

  • Shugaban Kungiyar kiristocin Nijeriya yayi kira ga Yan kudancin kasar dasu fito da wanda zai gaji Buhari a 2023
  • Ya bayyana hakane a jiya a wani liyafar da ya halarta a Ibadan
  • Ya yi kuma kira ga kiristocin kasar su bude idanuwansu wajen kada kuri'a a zaben dake tafe

Ibadan- Shugaban Kungiyar Kiristocin Nijeria, CAN, Rev. Samson Ayokunle, a jiya ya yi kira ga yan Nijeria musamman ma yan Kudancin Kasar da su fitar da Shugaban kasa kirista wanda zai ja ragamar Shugabanci a 2023.

Ayokunle ya bayyana haka ne a liyafar zagayowar ranar wani dakin taron hukumar cocin Christ Revival karo na 53 a Ibadan kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

A kalamensa:

"Ina so na yi kira ga dukkan Kiristocin dake dakin taron nan kuma na fada wa sauran yan Nijeriya cewa kuna kuka akan gurbataccen Shugabanci a Najeriya. Lokaci yayi da zaku chanza gurbatattun Shugabannin ku da kuri'arku.

"Kuna cewa bakwa san rashin shugabanci nagari a Nijeria, muna neman mutane kwararru wadanda zasu jagoranci Nijeria ta yadda mutane zasu ji dadi su nuna godiyarsu.

"Wannan wata dama ce garemu daga kuri'unku. Duk wanda bai amshi katin zaben shi ba to ya garzaya ya karba. Idan kana da matsala wajen karbar naka to ka fada mana.

2023: Lokaci yayi da Kudu zata fito da dan takarar Shugaban Kasa, CAN
2023: Lokaci yayi da Kudu zata fito da dan takarar Shugaban Kasa, CAN
Asali: Twitter

"Ba zaka zauna a gida ba kuma ka tsammaci Shugabanci nagari ba tare da ka zabi nagari ba. zaben shugaba nagari yana hannunka. ka amshi katin zaben ka akan lokaci.

Ba zamu sake bari mutanen banza su mulke mu ba

"Mutanen banza ba zasu kara mulkar Nijeria ba. Kar ka zabi mutum saboda yana da kudi ko ya shahara, ka zabi wanda yake da tsoron Allah a cikin rayuwarshi.

"Yan Arewa sun mulke mu na tsawon shekaru takwas kuma dukkansu musulmai ne. Saboda haka yanzu lokacin kirista ne da zai hau shima yayi shekaru takwas, saboda haka Allah yakeso, ya halicce mu kowa dai dai a Nijeriya.

"Mu kusan miliyan 200 ne a Nijeriya; kiristoci miliyan 100, musulmai ma miliyan 100.

"Ba zaka fada min cewa bayan shekaru 8 na mulkin dan Arewa musulmi, ba zaka samu kirista daya kwararre ba daga kudu cikin kiristoci miliyan 100 da zai iya hawa mulki ba na wasu shekaru takwas.

"Wannan shine wayan da zai sa kasa ta rayu idan aka ba dukka kabilu da addinai dama akan abubuwa, kuma yakamata kiristoci masu zabe su bude idanuwansu wajen kada kuri'a a wannan karon.

A wani labarin kuma Awanni 72 bayan rantsar da sabon shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya kama aikin Ofis ɗinsa gadan-gadan a Buhari House dake Sakatariyar APC ta ƙasa, Abuja.

Adamu, wanda ya ɗira harabar wurin da misalin ƙarfe 11:30 na safe ranar Laraba, ya samu kyakkyawan tarba daga dubbannin masoya, kamar yadda Punch ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel