Da Dumi-Dumi: Sabon Shugaban APC ya dira Sakatariyar jam'iyya ta ƙasa, ya kama aiki gadan-gadan
- Da misalin ƙarfe 11:30 na Safiyar Laraba, 30 ga watan Maris, shugaban APC na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu, ya isa Sakariyar jam'iyya
- Rahoto ya nuna cewa Adamu ya isa wurin ne tare da sauran mambobin kwamitin ayyuka NWC da aka zaɓa a wurin babban taron APC
- Wasu Hotuna da suka bayyana sun nuna yadda shugaba mai barin gado, Mala Buni, ya mika wa Adamu ragamar jagorancin jam'iyya
Abuja - Awanni 72 bayan rantsar da sabon shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu, ya kama aikin Ofis ɗinsa gadan-gadan a Buhari House dake Sakatariyar APC ta ƙasa, Abuja.
Adamu, wanda ya ɗira harabar wurin da misalin ƙarfe 11:30 na safe ranar Laraba, ya samu kyakkyawan tarba daga dubbannin masoya, kamar yadda Punch ta rahoto.

Asali: Twitter
Adamu ya isa Sakatariyar ne tare da sauran mambobin Kwamitin aiki na APC wato NWC domin fara aiki a kujerun da aka zaɓe su.

Kara karanta wannan
Da Dumi-Dumi: Gwamna Buni ya miƙa ragamar jam'iyyar APC hannun sabon shugaba na ƙasa
Shugaban jam'iyya mai mulkin ya shiga ganawa jim ƙaɗan bayan isarsa wurin, kuma wannan shi ne zuwansa na farko tun bayan ayyana shi a matsayin Ciyaman.
Buni ya miƙa masa ragamar APC
Sabon shugaban, a wani rubutu da Hotuna da ya saki shafinsa na Twitter, ya bayyana yadda Gwamna Buni ya mika masa jagorancin APC.
Ya kuma kara da cewa shugaban kwamitin rikon kwarya mai barin gado kuma gwamnan Yobe, Mai Mala Buni ya musu fatan Alheri.
Gwamnan jihar Neja, Abubakar Sani Bello, da sauran mambobin kwamitin ayyuka, sun shaida miƙa mulki hannun Adamu a Sakariyar APC dake birnin Abuja.
A wani labarin kuma Mutanen Gombe sun kai ƙarar Pantami Kotu kan neman takarar gwamna a zaɓen 2023
Wasu tawagar mutane a jihar Gombe sun maka Ministan Sadarwa, Isa Pantami a gaban Kotu kan kujerar gwamna.

Kara karanta wannan
Karin bayani: 'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, sun kashe 9 a jihar Neja
Shugaban ƙungiyar mutanen ya bayyana cewa sun ɗauki matakin ne domin tilasta masa ya nemi takarar gwamna a Gombe.
Asali: Legit.ng