Yanzu-Yanzu: Amaechi Ya Shiga Jerin Masu Son Ɗare Wa Kujerar Buhari a 2023

Yanzu-Yanzu: Amaechi Ya Shiga Jerin Masu Son Ɗare Wa Kujerar Buhari a 2023

  • Bayan an kwashe watanni ana yada jita-jira, ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya shiga cikin jerin ‘yan takaran shugaban kasa a zaben 2023
  • Duk da dai har yanzu bai riga ya bayyana hakan ba da bakinsa, amma ya yi wani jurwaye mai kama da wanka a cikin kwanakin karshen makon nan
  • An saki wani littafi wanda ya dinga yaba wa Amaechi tare da yin masa kamfen wanda yake nuna cewa gabadaya ci gaban kasar nan ta rataya a wuyansa

Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya shiga jerin ‘yan takaran shugaban kasa a zaben 2023 da ke karatowa bayan an kwashe watanni ana tsegunguma, Vanguard ta ruwaito.

Har yanzu dai bai fito a mutum ya bayyana cewa yana neman kujerar karara ba, amma an saki wani littafi a cikin kwanakin karshen makon nan wanda ya kambama shi.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya ya fadawa ‘Yan Najeriya su kauracewa zaben Atiku, Tambuwal, Saraki da Obi

Yanzu-Yanzu: Amaechi Ya Shiga Jerin Masu Son Ɗare Wa Kujerar Buhari a 2023
Yanzu-Yanzu: Amaechi Ya Shiga Jerin Yan Takarar Shugaban Kasa a 2023. Hoto: The Nation.
Asali: Facebook

An zabi jagoran jam’iyyar APC din, Amaechi har sau biyu, inda ya rike kujerar gwamnan Jihar Ribas a karkashin jam’iyyar PDP, amma kuma ya bar jam’iyyar kafin zaben 2015.

Ta yiwu PDP ta tsayar da dan takara daga kudu duk da tsohon gwaman Jihar Legas, Bola Tinubu, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da kuma Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi, sun nuna suna son kujerar shugaban kasa, kamar yadda Vanguard ta nuna.

Cikin littafin akwai hotunansa da Buhari da sauran manyan mutane

A jikin farkon fallen littafin mai feji 86, hoton Amaechi ne wanda aka rubuta, “Na yarda da cewa Najeriya za ta ci gaba ne matsawar ta zama kasa daya dunkulalliya. Abubuwan da muke bukata don kasarmu ta taso saboda kofofi su bude wa ‘yan Najeriya ba tare da wariyar yare, kudi ko kuma dama ba.”

Kara karanta wannan

Abba Kyari Ya Ƙi Cin Abincin Gidan Yari, 'Yan Gidan Yarin Suna Murna Da Zuwansa

A fejin karshe kuwa, an kara yin wani rubutu ne wanda aka alakanta shi da ministan inda aka ce, “wajibi ne mu yi demokradiyya mai kyau ta yadda ko wanne dan Najeriya zai samu wuri da kuma murya ba tare da bambanci ba tsakanin maza da mata. Wajibi ne mu gyara tudu da gangare, daji da gonaki yadda ‘yan Najeriya zasu iya ratsawa a ko yaushe.”

Sannan a cikin littafin akwai hotunan ministan sanye da kaya iri daban-daban na ‘yan Najeriya, hotonsa da matarsa, hotonsa da shugaba Muhammadu Buhari a wurare daban-daban, hotuna da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, shugaban RCCG, Fasto Enoch Adeboye da kuma farfesa Yemi Osinbajo.

An kambama Amaechi a cikin littafin

A fejin littafin na uku akwai sunan ministan a rubuce wanda aka fassara shi da turanci a matsayin Chibuike - Ubangiji ne karfinmu; Rotimi - Ku kasance tare da ni da kuma Amaechi - Wa ya san me gobe za ta haifar.

Kara karanta wannan

Gwamna Yahaya Bello ya bayyana wanda ya kamata ya gaji Buhari a zaben 2023

Littafin ya kunshi bayanai kamar 'Zaben nagari; dalilin dayasa; Halayen Chibuike Rotimi Amaechi na kwarai; Gogewarsa a harkar mulki; Dubin da yake yi wa kasa; Rayuwarsa da salon shugabancinsa; Nasarorinsa: Gwamnan Jihar Ribas daga 2007 zuwa 2015; Nasarorinsa: Ministan sufuri (2015 zuwa yanzu) da sauransu.'

Cikin halayensa da aka lissafo akwai jajircewa da dagewa da sauransu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel