Innalillahi: Ba a gama jimamin harin jirgin kasa ba, 'yan bindiga sun hallaka mutum 23 a Kaduna

Innalillahi: Ba a gama jimamin harin jirgin kasa ba, 'yan bindiga sun hallaka mutum 23 a Kaduna

  • Bayan da aka samu harin 'yan bindiga a jihar Kaduna cikin makwannin, lamura na kara tabarbarewa
  • An samu sabon harin 'yan bindiga, inda aka hallaka mutane har 23 nan take a wani yankin Giwa na jihar
  • Rahotanni da muke samu sun bayyana cewa, ya zuwa yanzu dai gwamnati bata ce komai akai ba

Giwa, Kaduna - Wasu ‘yan bindiga sun sake kashe wasu mutane 23 tare da raunata wasu da dama a wasu kauyuka biyu na karamar hukumar Giwa a jihar Kaduna.

Wannan dai shi ne hari na hudu a jere da ‘yan bindiga suka kai a cikin mako guda a kauyukan karamar hukumar, Daily Trust ta ruwaito.

Kauyukan da ‘yan bindigar suka kai hari sun hada da Anguwar Maiwa da Anguwar Kanwa.

Innalillahi: Ba a gama jimamin harin jirgin kasa ba, 'yan bindiga sun hallaka mutum 23 a wani yankin jihar Kaduna
Innalillahi: Ba a gama jimamin harin jirgin kasa ba, 'yan bindiga sun hallaka mutum 23 a Kaduna | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wani ganau ya ce ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyukan ne da misalin karfe 1:00 na daren ranar Talata.

Kara karanta wannan

Yadda Rahama Sadau da ‘Yaruwarta suka taki sa’a, saura kiris harin jirgin kasa ya rutsa da su

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya bayyana cewa:

“An ga ‘yan bindigar suna taruwa a kan babura tun da yammacin ranar Litinin da karfe 5 na yamma kuma an sanar da jami’an tsaro.
"Duk da haka, 'yan bindigar sun ci gaba, suka aikata barnar su."

Wani ganau ya ce an gano gawarwaki 22 tare da taimakon jami’an tsaro daga cikin 23 da aka ce an kashe kuma aka binne su.

Ya ce jami’an tsaro sun kuma yi nasarar kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar tare da kwato wasu da aka yi garkuwa da su, hakan Daily Post ta tattaro.

A cewarsa:

"Ba zan iya cewa ga adadin wadanda aka ceto ba, amma na san an kubutar da wasu daga cikinsu kuma an kashe 'yan bindiga."

Har yanzu dai ba a samu jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalinge ba.

Kara karanta wannan

Bayanin rundunar soja: Mutum 7 sun mutu, 29 sun jikkata a harin jirgin kasan Abuja-Kaduna

Wata sabuwa: Ƴan sanda sun daƙile harin da miyagu suka kai matatar man fetur ta Ɗangote

A wani labarin, jami'an tsaro sun bankaɗo yunƙurin kai farmaki matatar man fetur ta Dangote, dake Lekki Free Trade Zone cikin jihar Legas.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fita ranar Talata.

Ya ce, an daƙile harin da hatsabiban suka yi yunkurin kaiwa ne, yayin kokarin awon gaba da keburan karfen da aka riga aka saka cikin matatar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel