Wata sabuwa: Ƴan sanda sun daƙile harin da miyagu suka kai matatar man fetur ta Ɗangote

Wata sabuwa: Ƴan sanda sun daƙile harin da miyagu suka kai matatar man fetur ta Ɗangote

  • Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Legas ya tabbatar da yadda ƴan bindiga suka yi kokarin kai farmaki matatar Dangote, Lekki Free Trade Zone cikin jihar
  • Jami'an tsaro sun yi nasarar daƙile harin da hatsabiban suka yi yunkurin kaiwa, yayin kokarin awon gaba da wasu keburan ƙarfe da aka sanya a matatar
  • Yayin kai farmakin, an gano yadda jami'an tsaro suka buɗewa ɓarayin wuta, wanda yayi sanadiyyar sheƙawar ɗaya daga cikin ƴan bindigan lahira

Legas - Jami'an tsaro sun bankaɗo yunƙurin kai farmaki matatar man fetur ta Dangote, dake Lekki Free Trade Zone cikin jihar Legas.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar Legas, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da hakan a wata takarda da ya fitar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Abun Kunya: Wani Magidanci ya ɗirka wa ɗiyarsa ciki har sau biyu, ya saki Matarsa ta Sunnah

Wata sabuwa: Ƴan sanda sun daƙile harin da miyagu suka kai matatar man fetur ta Ɗangote
Wata sabuwa: Ƴan sanda sun daƙile harin da miyagu suka kai matatar man fetur ta Ɗangote. Hoto daga Vanguardngr.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda kakakin ya bayyana, harin ya auku ne a safiyar Litinin, Vanguard ta ruwaito.

Ya ce, an daƙile harin da hatsabiban suka yi yunkurin kaiwa ne, yayin kokarin awon gaba da keburan karfen da aka riga aka saka cikin matatar.

"An yi nasarar dakile harin hatsabiban da zasu kai su 20, waɗanda suka samu damar shiga matatar ta ɓangaren ruwa.
"Sun ranta a na kare, yayin da suka yi ido biyu da jami'an tsoro a wurin."

Hundeyin ya bayyana yadda ɗaya daga cikin hatsabiban ya rasa ransa.

"Yayin luguden wutar, an yi nasarar sheƙe ɗaya daga cikin ɓarayin, wanda ya sheƙa barzahu a kan hanyar kai shi asibiti.
"A halin yanzu ana bincikar lamarin, don damƙo ƴan fashin da suka kai farmakin.
"Bisa umarnin kwamishinan ƴan sandan jihar Legas, CP Abiodun Alabi, an tabbatar da tsaro a matata," a cewarsa.

Kara karanta wannan

Alwan Hassan, Manajan Daraktan BOA, ya yi batan dabo ta harin jirgin kasan Kaduna-Abuja

Yadda sojoji suka kwace iko a filin jirgin Kaduna daga harin da ‘yan ta’adda suka kai kan na’urori

A wani labari na daban, a ranar Asabar din da ta gabata ne ‘yan ta’addan da yawansu ya kai 200 suka dire filin jirgin sama na Kaduna da ke karamar hukumar Igabi a Kaduna, inda suka dakile aiki tare da kashe jami’in tsaro daya na hukumar kula da sararin samaniyar Najeriya.

Harin ya haifar da tashin hankali a filin jirgin, inda rahotanni suka ce an hana jirgin AZMAN da ke kan hanyar Legas ya tashi da karfe 12:30 na rana.

Majiyoyi a hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya sun shaidawa jaridar Sunday Punch cewa, ‘yan ta’addan sun kai hari a wurin da kayan aikin VHF a filin jirgin suke kuma sun kashe wani jami’in tsaro da ke gadin wurin.

Harin, an tattaro cewa, ya tilastawa mahukuntan filin tashi da saukar jiragen saman rufe harkokin na wani dan lokaci, yayin da sojoji ke fafatawa da wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Bayan kashe mutum 50, 'Yan bindiga sun sake sheƙe dandazon mutane a Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng